Coronavirus: Kasar Iran ta mayar da Masallaci kamfanin hada takunkumin fuska

Coronavirus: Kasar Iran ta mayar da Masallaci kamfanin hada takunkumin fuska

- Kasar Iran ta mayar da wani babban masallaci da ke Tehran kamfanin hada takunkumin fuska

- Matan da ke kai dauki ga baki a filin yaki ne suke dinka takunkumin don bada gudumawar yakar annobar coronavirus

- Kamar yadda daya daga cikinsu ta bayyana, wannan aikin da take yi tamkar faranta zuciyar Imamu Mahdi ne wanda suke kira da Imamu Zaman

Wani masallaci da ke garin Tehran an mayar dashi kamfanin hada takunkumin fuska. Mata kuwa masu aikin sa kai wadanda ke kula da baki a tsohon filin yaki na Iran-Iraq sun hada kai wajen yakar annobar coronavirus.

Mata kusan 15 ne ke jere a kan kekuna suna samar da takunkumin fuska. Dukkansu kuwa 'yan kungiyar sa-kai ce ta Basij, kungiya ce wacce ke biyayya ga dokokin musulunci na Iran.

Coronavirus: Kasar Iran ta mayar da Masallaci kamfanin hada takunkumin fuska

Coronavirus: Kasar Iran ta mayar da Masallaci kamfanin hada takunkumin fuska
Source: Facebook

Sakamakon barkewar muguwar annobar coronavirus a kasar Iran, dukkan matan na saka takunkumin fuska, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

"Kungiyar mu tana zuwa filin yaki kowacce shekara don aiki ga baki," Fatemeh Saidi, mai shekaru 27 da ke cikin kungiyar Basij tare da mijinta ta sanar da AFP.

Kungiyar matan sama da 40 na zuwa filin yaki ne duk shekara tun daga 1980 zuwa 1988 wanda matasa ke kawo ziyara yayin hutun sabuwar shekara na kasar Fasha.

"A wannan shekarar, an haramta yawo tsakanin birane da garuruwa sakamakon annobar coronavirus da ta barke," Saidi tace.

"Mun zo taimakon 'yan uwanmu. Mun fara aikin nan kusan wata daya kenan," ta kara da cewa.

Wannan aikin suna ganin shi ne iyakar kokarin da za su iya yi wa kasarsu don tallafawa yakar cutar coronavirus wacce ta lamushe rayuka 3,700 a Iran.

KU KARANTA: Karya suka shara mini, ban ce babu yunwa a Najeriya ba - Lai Mohammed ya koka kan masu yada labaran shi na bogi

"Lamarin mu ya kasance mai tsauri tunda muna fuskantar hukunci ne da kuma coronavirus," shugaban kasa Hassan Rouhani ya ce a ranar Litinin, yayin da yake magana a kan takunkumin da Amurka ta sake sanyawa Iran tun bayan janye yarjejeniyarta da ita a 2018.

Manema labaran kasar da na kasashen ketare duk sun amsa gayyatar Imamzadeh-Masum zuwa masallacin da ke kudu maso yamma na babban birnin Iran din inda mata ke aikin.

Kamar yadda aka gani, wasu na yanka ne kuma suna zubawa a bokiti. Sauran matan na ninkewa tare da daidaita yadin. A wani daki na daban, maza ne ke hada safar hannu.

"Muna raba kayayyakin nan ne ga asibitoci da kuma wasu sassan kasar nan," Saidi tayi bayani.

Daya daga cikin masu aikin ta bayyana mahangar wannan taimakon da take a addinance. Gareta, tamkar farantawa zuciyar Imamu Zaman ne, sunan da suke kiran Mahdi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel