Zamanin biyan kudin tallafin man fetir ya kare a Najeriya – Kyari

Zamanin biyan kudin tallafin man fetir ya kare a Najeriya – Kyari

Alamu sun nuna gwamnatin tarayya ta kawo karshen wa’adin biyan kudaden tallafin man fetir musamman duba da ragin da aka samu a kan farashin litar mai daga N145 zuwa N123, inji rahoton Daily Trust.

Wannan alamu sun bayyana ne daga jawabin da shugaban kamfanin man fetir ta Najeriya, NNPC, Malam Mele Kyari ya yi yayin da ya bayyana cikin wani shirin gidan talabijin na AIT mai suna ‘Moneyline’, inda yace gwamnati ta zare tallafin man fetir gaba daya.

KU KARANTA: Habbatissaudah da zuma ne suka warkar da ni daga Coronavirus – Gwamna Makinde

Zamanin biyan kudin tallafin man fetir ya kare Najeriya – Kyari
Zamanin biyan kudin tallafin man fetir ya kare Najeriya – Kyari
Asali: UGC

“Abin da nake nufi shi ne zuwa nan gaba kadan, babu sauran maganan kudin tallafi, NNPC za ta zama tamkar sauran yan kasuwa ne, kasuwanci kawai za’a yi.” Inji shi.

A ranar Laraba, 18 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya ta rage naira tiriliyan 1.5 daga cikin kasafin kudin shekarar 2020 da ya kai naira tiriliyan 10.59, a matsayin wani mataki na rage hidimar da gwamnatin za ta yi.

Haka zalika gwamnatin ta rage farashin litar man fetir, tare da umartar hukumar dake kula da daidaita farashin mai ta cigaba da juya akalar farashin man fetir duba da yanayin sauye sauyen da ake samu a kasuwar mai.

A shekarar 2019 kadai, gwamnatin tarayya ta kashe kimanin naira biliyan 780 wajen biyan tallafin man fetir, yayin da a kasafin kudin shekarar 2020 ta kiyasta kashe kimanin naira biliyan 450. Tun a shekarar 2015 gwamnatin Buhari ke biyan tallafi, musamman bayan ta kara farashin mai daga N97 zuwa 145.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cire dala miliyan 150, kimanin naira biliyan 55 daga asusun kasa na musamman wanda aka fi sani da suna ‘Sovereign Wealth Fund’.

Shugaban ya amince a cire kudin ne domin raba ma matakan gwamnatin tarayya, jahohi da kuma na kananan hukumomi sakamakon bullar annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja yayin da take ganawa da manema labaru game da matakan da gwamnati take dauka don rage radadin Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel