Yanzu Yanzu: Jahar Ogun ta samu sabbin mutane 2 da suka kamu da coronavirus
- An sake samun sabbin mutane biyu da suka kamu da cutar coronavirus a jahar Ogun
- A yanzu jumlar mutane shida kenan suka kamu a jahar
- Daya daga cikinsu ya zo daga Mowe a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jahar, inda dayan ya fito ne daga karamar hukumar Yewa ta Kudu
Rahotanni daga jaridar The Nation sun kawo cewa an sake samun sabbin mutane biyu da suka kamu da cutar Covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus a jahar Ogun. A yanzu jumlar mutane shida kenan suka kamu a jahar.
Gwamna Dapo Abiodun, wanda ya bayyana hakan a gidansa da ke Iperu, jahar Ogun yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu, ya ce wadanda suka kamun basu da wani tarihi na zuwa kasashen da annobar coronavirus ya barke kuma ba su hadu da mutanen da suka yi tafiya ba.
Abiodun ya ce wannan sabon lamari a jahar ya nuna cewa cutar baya la’akari da matsayi, shekara, jinsi ko kuma asalin mutum.
Ya ce yayinda daya ya zo daga Mowe a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jahar, dayan ya fito ne daga karamar hukumar Yewa ta Kudu.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus na farko a jihar Kwara
A wani labarin kuma, mun ji cewa a yayinda jihar Kaduna ta samu karin mai cutar Coronavirus daya ranar Lahadi, wanda ya kai adadin masu cutar a jihar 5, gwamnatin jihar ta ce kawo yanzu an tura sanfurin jinin mutane 89 Abuja domin gwaji.
Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Amina Mohammed Baloni, wacce ta bayyana hakan ranar Litinin ta ce cikin samfura 89 da aka tura, sakamakon ya nuna 5 sun kamu, 77 basu kamu ba, kuma ana sauraron 8.
Baloni a jawabin da ta saki ranar Litinin ta ce kawo yanzu an katabta sunayen mutane 119 da ake nema.
Tace: "Gwamnatin jihar na dauka tsauraran matakai wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 tun watan Febrairu ta hanyar tuntubar shugabannin asibitocin jihar kan yadda za'a shawo kan lamarin."
"Mun karfafa cibiyar takaita yaduwar cututtukan (dake jihar) ta hanyar tura kwararrun ma'aikata wajen masu kula da marasa lafiya yanzu."
"Bugu da kari, ma'aikatar ta kammala shirin samar da gidan killace mutane mai dakuna 69 domin ajiye wadanda cutan ya fara bayyana jikinsu."
"Ana kyautata zaton za'a bude wajen wannan makon."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng