Wani mutumi ya bindige mutane 5 sakamakon sun dame shi da surutu
Yawan surutu mara kan gado tare da daga murya ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane biyar har lahira a kasar Rasha, bayan da wani mutumi yace sun dame shi.
BBC Hausa ta ruwaito yan zaman majalisar su biyar da suka hada da maza hudu da mace daya suna hirarsu ne a kofar gidan wannan mutumi da daddare, a kauyen Yelatma dake yankin Ryazin na kasar Rasha.
KU KARANTA; Annobar Coronavirus: Buhari ya zari dala miliyan 150 daga wani asusun Najeriya
Wannan mutumi da ba’a bayyana sunansa ba ya gargadi mutanen game da damunsa da suke yi da surutunsu daga saman benensa, amma sai suka mayar masa da martani, wanda hakan ya yi sanadiyyar kaurewar hayaniya a tsakaninsu.
Ba tare da wata wata ba, sai gogan naku sarkin fushi ya shiga cikin ya fito da bindigar farauta, inda ya dinga yi ma yan majalisar nan su biyar dauki dai dai, toh da yake yankin na killace saboda annobar Coronavirus, koda aka mika su asibiti tuni sun rigamu gidan gaskiya.
Yansandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka ce ya faru ne da misalin karfe 10 na daren Asabar, kuma a yanzu haka sun kama sarkin fushin, sa’annan sun kwace bindigarsa.
A wani labari kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa sun daina bayyana irin shirin da suka tanadar ma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, don haka zai kasance sirri ne.
Daily Trust ta ruwaito Buratai ya bayyana haka ne a yayin taron cin abincin dare da rundunar ta shirya don karrama tsohon kwamandan yaki da Boko Haram na Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi a garin Borno.
Buratai ya bayyana cewa rundunar ba za ta sake fallasa shirinta ba, amma ya yi kira ga dakarun rundunar Sojin kasa da su kasance cikin shiri domin kuwa akwai aiki na musamman da za su gudanar nan bada jimawa ba.
“Ba za mu fadi shirye shiryen mu ba, amma na san da zarar kun fara natsuwa a aikin, babban aiki zai same ku, kuma dukkanin sabbin kwamandojin su shirya akwai aiki a gabansu.” Inji Buratai ga sabon kwamandan Manjo Janar Farouk Yahaya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng