Kasar Ghana za ta kara wa ma’aikatan jinya kaso 50 na albashi da kuma yafe wa mutane kudin ruwa

Kasar Ghana za ta kara wa ma’aikatan jinya kaso 50 na albashi da kuma yafe wa mutane kudin ruwa

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar da wasu shirin tallafi da ta tanadar wa al’ummanta domin rage masu radadin lamura sakamakon annobar coronavirus. Ta kuma yi wa ma’aikatan lafiya wadanda sune kan gaba wajen yakar annobar tanadi na musamman.

A wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar ta gidajen talbijin a ranar Lahadi, 5 ga watan Afrilu,shugaba Nana Akufo-Addo ya ce gwamnatinsa za ta biya a al’ummanta kudin ruwa na watannin Afrilu, Mayu da kuma Yuni.

Tallafin gwamnatin na zuwa ne a tsaka da lokacin da ake korafin cewa wasu garuruwa basa da ruwan famfo wanda shine matakin tsira na wanke hannu da aka ce a dunga yi a kokarin hana kamuwa da cutar ta Covid-19.

Kasar Ghana za ta kara wa ma’aikatan jinya kaso 50 na albashi da kuma yafe wa mutane kudin ruwa

Kasar Ghana za ta kara wa ma’aikatan jinya kaso 50 na albashi da kuma yafe wa mutane kudin ruwa
Source: Facebook

Shugaban kasar ya ce gwamnati na tattaunawa da ma’aikatun rowan tanka su zaman kansu domin su dunga kai wa garuruwa ruwa domin amfanin kansu.

Ya kuma ba al’umman kasar tabbacin samun wutar lantarki mai karko.

Akufo-Addo ya kuma sanar da cewar dukkanin ma’aikatan lafiya da ke kan gaba wajen warkar da masu cutar COVID-19 za su samu Karin kaso 50 na albashi sannan kuma cewa ba za su biya haraji ba a watanni uku masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Mutane 119 da muke nema yanzu - Gwamnatin jihar Kaduna

A gefe guda mun ji cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cire dala miliyan 150, kimanin naira biliyan 55 daga asusun kasa na musamman wanda aka fi sani da suna ‘Sovereign Wealth Fund’.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban ya amince a cire kudin ne domin raba ma matakan gwamnatin tarayya, jahohi da kuma na kananan hukumomi sakamakon bullar annobar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus.

Ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ranar Litinin, a babban birnin tarayya Abuja yayin da take ganawa da manema labaru game da matakan da gwamnati take dauka don rage radadin Coronavirus.

Ministar ta bayyana cewa za’a cire kudaden ne don cike gibin da aka samu sakamakon karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwan duniya, inda tace tun daga watan Janairun kudaden shigar gwamnati ke yin kasa, wanda hakan ya shafi kudaden da ake rabawa tsakanin matakan gwamnatocin uku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel