Tsohon Firayim Ministan kasar Libya, Mahmoud Jibril ya mutu a Masar

Tsohon Firayim Ministan kasar Libya, Mahmoud Jibril ya mutu a Masar

Mahmoud Jibril, wanda ya jagoranci gwamnatin tawaren da ta kifar da dadadden shugaban Libya, Muammar Gaddafi a 2011, ya kwanta dama bayan fama da cutar COVID-19.

Aljazeera ta fitar da rahoto cewa Mahmoud Jibril mai shekaru 68 a Duniya ya rasu ne a wani asibitin kasar Masar. Jibril ya yi jinya a asibitin na kusan tsawon makonni biyu.

Khaled al-Mrimi wanda shi ne babban Sakataren jam’iyyar National Forces Alliance da tsohon shugaba Mahmoud Jibril ya kafa a shekarar 2012, ya shaidawa Duniya wannan.

Khaled al-Mrimi ya ce Mahmoud Jibril ya cika ne a wani asibitin kwararru mai suna Ganzouri a Masar. Jami'an Asibitin sun ce zuciyar Jibril ce ta buga a Ranar 21 ga Watan Maris.

Bayan an kai shi asibiti, sai aka tabbatar da cewa ya kamu da Coronavirus. shugaban wannan asibiti, Hisham Wagdy ya ce jikin Jibril ya tabarbare ne bayan ya fara samun sauki.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Sokoto ta dauki matakan yakar cutar COVID-19

Tsohon Firayim Ministan kasar Libya, Mahmoud Jibril ya mutu a Masar
Mahmoud Jibril ya taba rike kujerar Firayim Minista a kasar Libya
Source: Facebook

Hisham Wagdy ya fadawa AFP cewa: “Ya fara murmurewa a shekaran jiya (Juma’a), sai kuma jikinsa ya rikici.” A Ranar Lahadi da rana tsake ne Dattijon ya ce ga garinku nan.

An killace tsohon Firayim Ministan ne a asibitin bayan an gano cewa ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. Jibril ya yi jinya a sashen da ake kula da wanda jikinsu ya yi kamari.

Mahmud Jibril ya yi aiki a gwamnatin Gaddafi a matsayin Mai bada shawara a kan harkar tattalin arziki. A 2011 ne Jibril ya shiga cikin ‘Yan tawaye da su ka kifar da gwamnati.

Ba wannan ba ne karon farko da cutar Coronavirus ta kashe tsohon shugaban kasar Afrika. Idan ba ku manta ba tsohon shugaban Somaliya Nur Hassan Husseini ya mutu kwanaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel