UK: Annobar Coronavirus ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 620 a rana guda
A daidai lokacin da ake kuka game da yadda cutar COVID-19 ta hallaka mutane fiye da 350 a Ranar Asabar, a Faransa, sai kuma aka ji wani mummunan labari ya fito daga Birtaniya.
Rahotanni sun bayyana cewa akalla ba a kasara ba, mutane fiye da 600 su ka kwanta dama a sanadiyyar cutar COVID-19 a Ingila. Wannan ya faru ne a Ranar 4 ga Watan Maris, 2020.
A Ranar Asabar din, mutane kimanin 5, 900 ne aka samu labarin cewa sun kamu da COVID-19. Sakamakon gwajin da aka yi a wannan rana ya nuna masu cutar sun karu da mutum 5, 903.
A jiya da kusan karfe 2:00 na rana, BBC ta fitar da rahoton an samu karin mutanen da wannan cuta mai jawo wahalar numfashi ta kashe. A Ranar Juma’a mutum 4, 300 ne su ka mutu.
Kawo yanzu cutar Coronavirus ta kashe mutane 4, 934 a kasar Ingila. Wannan ya sa Ingila ta shiga cikin sahun Italiya, Sifen, Amurka, Iran da China, inda annobar ta fi kamari a Duniya.
KU KARANTA: COVID-19: Likitocin Najeriya su na da ja game da agaji daga kasar Sin
An fara samun wanda Coronavirus ta kashe ne a Ingila a tsakiyar Watan Maris. A cikin ‘yan makonnin da su ka biyo baya annobar ta yi kamari, inda ta yi sanadiyyar mutuwar dubannai.
Tsakanin Juma’a zuwa Asabar, fiye da mutane 1, 380 wannan cuta ta hallaka a Ingila. Bayan haka kuma akwai masu jinya 1, 559 da Likitoci su ka bayyana cewa sun shiga halin gargara.
Kasar Ingila ta yi rashin sa’ar kamuwa da wannan cuta da ta bullo daga Sin a karshen bara. Alkaluma sun nuna cewa akwai mutane kusan 48, 000 da ke dauke da COVID-19 a kasar.
Ana tsakiyar wannan ne kuma mu ka samu labari cewa an tafi da Firayim Ministan kasar ta Birtaniya, Boris Johnson, asibiti domin sake yi masa gwaji bayan ya kamu da COVID-19.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng