Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojinsa zuwa rumbun makaman Boko Haram a Sambisa (Hotuna)

Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojinsa zuwa rumbun makaman Boko Haram a Sambisa (Hotuna)

Sojojin kasar Chadi sun kama wasu makamai masu dumbin yawa a wata maboya da ake kyautata zaton rumbun ajiyar makaman mayakan kungiyar kungiyar Boko Haram ne da ke cikin dajin Sambisa.

A ranar Asabar ne dakarun sojin kasar Chadi suka fara wani atisayen ba mutunci a kan mayakan kungiyar Boko Haram a yankin Goje zuwa yankin kasar Chadi a cikin dajin Sambisa, hedikwatar Boko Haram.

Sojojin kasar Chadi sun shafe sa'o'i kimanin hudu suna farautar mayakan kungiyar Boko Haram a wani atisaye da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya jagoranta.

Deby tsohon shugaban rundunar sojojin kasar Chadi ne.

Wata majiya daga cikin sojoji ta shaidawa jaridar 'The Cable' cewa rumbun makaman da sojojin suka gano shine mafi girma da kungiyar Boko Haram ke gadara da shi.

DUBA WANNAN: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

Da yake magana a kan atisayen, Deby ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa, "Na ziyarci Baga-Sola domin ganin sojojin da suka samu raunuka sakamakon zazzafan atisayen da aka kaddamar a kan mayakan kungiyar Boko Haram. Sun samu rauni a yayin da suke hidmtawa kasarsu.

"An kawar da daruruwan mayakan Boko Haram kafina a kai ga cimma wurin da rumbun makaman ya ke," a cewar wata majiyar.

A yayin da yake ganawa da kwamandojin rundunar sojojin hadin gwuiwa (MNJTF) a Baga ta jihar Borno bayan harin daka kai wa sojojin kasarsa, shugaban kasar Chadi, Idriss Derby, ya bawa sojojin umarnin su fara wani atisaye, ba tare da nuna tausayi ba, a yankin tafkin tekun Chadi.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu, an ga sojojin kasar Chadi suna wakokin karawa junansu karfin gwuiwa yayin da suke harbawa mayakan kungiyar Boko Haram makami mai nisan zango (RPG) a lokacin da suke kazamar musayar wuta.

Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojinsa zuwa rumbun makaman Boko Haram a Sambisa (Hotuna)

Sojojin kasar Chad sun tattaro makan 'yan Boko Haram
Source: Twitter

Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojinsa zuwa rumbun makaman Boko Haram a Sambisa (Hotuna)

Shugaban kasar Chadi a sansanin sojoji a Sambisa
Source: Twitter

Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojinsa zuwa rumbun makaman Boko Haram a Sambisa (Hotuna)

Shugaban kasar Chadi a Sambisa
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel