Yanzu ba na dauke da kwayar cutar covid-19 - Gwamna Makinde

Yanzu ba na dauke da kwayar cutar covid-19 - Gwamna Makinde

Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya sanar da cewa sakamakon gwajinsa na biyu ya sake nuna cewa yanzu ba ya dauke da kwayar cutar covid-19.

Gwamna Makinde ya sanar da hakan ne a daren ranar Lahadi a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

A cikin sanarwar, gwamnan ya mika godiyarsa ta musamman ga mutanen jiharsa bisa damuwar da suka nuna a kansa tare da yi masa addu'o'in samun lafiya.

"Na ji dadin yadda kuka nuna goyon bayanku gareni tare da yi min addu'o'i, ina mai godiya kwarai a gareku. A yammacin nan na sake karbar sakamakon gwajin kwayar cutar covid-19 na biyu da aka sake yi min, wanda kuma ya kara tabbatar da cewa bana dauke da kwayar cutar. Ina mika godiya ta musamman ga Farfesa Temitope Alonge, mutumin da ya wakilceni a jagoranci kwamitin ko ta kwana na yaki da annobar cutar covid-19 a jiahr Oyo lokacin da nake killace," a cewar gwamnan.

A ranar Litinin, 30 ga watan Maris, ne gwamna Makinde ya sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar covid-19. Ya sanar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

DUBA WANNAN: Covid-19: Trump ya yi wa Amurkawa mummunan albishir din abinda zai faru sati mai zuwa

"Yanzunnan na samu sakamakon gwajin tabbatarwa da ke nuna cewa ina dauke da kwayar cutar covid-19. Babu wasu alamu da ke nuna cewa ba ni da koshin lafiya, amma duk da haka zan killace kaina tare da cigaba da samun kulawa," kamar yadda ya bayyana a wancan lokacin.

Makinde ne gwamna na biyu da ya samu waraka daga cutar covid-19 a tsakanin manyan jami'an gwamnati da suka kamu da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng