Yan sanda sun kama Funke Akindele kan shirya liyafa a gidanta a yayinda aka hana fita

Yan sanda sun kama Funke Akindele kan shirya liyafa a gidanta a yayinda aka hana fita

- An kama shararriyar yar wasar kudu Funke Akindele-Bello kan shirya liyafar zagayowar ranar haihuwa a gidanta a lokacin da dokar hana fita ke aiki

- Mijin yar wasar ya kara shekara daya a duniya a ranar Asabar sannan ma’auratan suka gayyaci abokansu wanda yan Najeriya suka ce sun fi yawan adadin mutanen da gwamnati ta amince da su a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus

- Rundunar yan sandan jahar Lagas sun shawarci mijin yar wasar da mawaki Naira Marley su kai kansu ofishinsu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu ko kuma a sanya su cikin wadanda ake nema ruwa a jallo

Yan sandan jahar Lagas sun kama shahararriyar yar wasar kudu wato Nollywood, Funke Akindele-Bello kan shirya liyafa a gidanta domin murnar zagayowar ranar haihuwar mijinta a ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu a Amen Estate.

A bisa ga wani jawabi daga rundunar yan sandan jahar Lagas dauke da sa hannun DSP Bala Elkana, kakakin yan sandan jahar, ya ce jami’an rundunar daga sashin CID Yaba ne suka kama yar wasar Jenifa.

Yan sanda sun kama Funke Akindele kan shirya liyafa a gidanta a yayinda aka hana fita
Yan sanda sun kama Funke Akindele kan shirya liyafa a gidanta a yayinda aka hana fita
Source: Instagram

Yayinda aka kama yar wasar kan lokaci, ba a ga maigidanta, JJC Skillz da Naira Marley ba sannan yan sandan suka shawarce su da su kai kansu ofishinsu a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilu ko kuma a kaddamar da su cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da mutuwar wani mai coronavirus a jahar

A wani labarin kuma mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas a ranar Lahadi ta sanar da cewa an sake sallamar mutane biyar masu cutar Coronavirus bayan samun waraka a asibitin jinyar cututtuka dake unguwar Yaban jihar.

Gwamnan jihar Legas da kansa, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Lahadi, 5 ga watan Afrilu, 2020.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Legas, a jiya (Asabar) na sanar muku cewa mun sallami mutum daya daga asibitin jinyar cututtuka dake Yaba. A yau Ina farin cikin sanar muku cewa mutane biyar (maza biyu da mata uku) cikin akwai wani dan shekara 10 da haihuwa sun samu waraka daga cutar #COVID19."

"Tuni a mayar da wadannan mutane biyar wajen iyalansu. Yanzu jimillan mutane 29 suka samu waraka tare da sallama a asibitinmu dake Yaba."

"Duk da cewan akwai alamun nasara kan cutar COVID-19, ya kamata mu zange dantse wajen takaita yaduwarta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel