Hukumomi za su dauki matakin duba lafiyar wadanda su ka shigo Sokoto daga ketare
Idan ba a manta ba, kwanan nan mu gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya fadada kwamitin yaki da COVID-19 a jihar Sokoto domin hana wannan cuta yaduwa a cikin jihar.
Domin hana yaduwar cutar COVID-19, a jihar Sokoto, gwamnati ta bayyana cewa za ta fara yawo daga gida zuwa gida domin binciken wadanda su ka yi tafiya kwanan nan.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Hum Angle, gwamnatin jihar Sokoto za ta rika binciken wadanda su ka ziyarci kasashen ketare inda da wannan cuta ta yi kamari.
Haka zalika gwamnatin jihar ta bakin Ma’aikatar kiwon lafiya ta ce, za ta sa ido ga Bayin Allah da su ka kai ziyara zuwa jihohin Najeriya da cutar ta Coronavirus ta shiga.
Mai girma Kwamishinan lafiyan, Muhammad Ali Inname, ya bayyana cewa duk da babu wanda ya kamu da wannan cuta a jihar, su na daukar matakan kare Bayin Allah.
KU KARANTA: Annobar COVID-19 ta sa kamfanoni za su fara sallamar Ma'aikata
Kwamishinan ya sanar da wannan ne wajen wani zama da ya yi da kwamitin da aka kafa na musamman domin yaki da cutar COVID-19 tare da bada agajin gaggawa.
Wadanda su ka halarci wannan zama da Dr. Ali Inname sun hada da daukacin Darektocin ma’aikatar kiwon lafiya da ke fadin kananan hukumomi 23 na jihar Sokoto.
Dr. Inname ya ce jihar Sokoto za ta hada-kai da sauran hukumomi domin bin duk wadanda su ka shigo jihar daga kasashen da wannan cuta ta ratsa, ko kuma jihohin kasar.
Inname ya ke cewa gwamnati za ta rika duba wadannan mutane domin ta tabbatar cewa ba su dauke da wannan cuta. Wannan zai taimaka wajen rage yaduwar Coronavirus.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng