Covid-19: Trump ya yi wa Amurkawa mummunan albishir din abinda zai faru sati mai zuwa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fadawa Amurkawa su zama cikin shirin ganin kara tsamarin cutar covid-19 a kasar, a yayinda jama'a da dama ke kara kamuwa wasu kuma suna mutuwa saboda annobar.
"Mutane da yawa za su kara mutuwa," shugaba Trump ya fada yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron manema labarai ranar Lahadi.
Kazalika ya mayar da martani a kan sukar da wasu gwamnoni ke yi wa gwamnatin tarayya a kan rashin samar da isassun na'aurar taimakon numfashi (ventilators) ga masu fama da cutar covid-19 a jihohinsu.
A cewar Trump, wasu daga cikin gwamnonin na neman adadin na'urar da basa bukata.
"Tsoron kar na'urar ta kare yasa suke kara yawan adadin da ya kamata su nema," a cewarsa.
Sannan ya cigaba da cewa, "wani lokaci da yafi wannan muni yana nan tafe.
"Ba na jin mun taba fuskantar yanayi irin wannan na mutuwar mutane masu yawa. Watakila tun bayan yakin duniya na daya ko na biyu."
A ranar Asabar ne Trump ya bayyana cewa ba zai iya rufe fuska da takunkumi ba duk da sabuwar dokar kare lafiya a kasar Amurka ta bawa 'yan kasar shawarar amfani da takunkumin domin kare kansu daga kamuwa da kwayar cutar covid-19.
DUBA WANNAN: Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a
A cewar shugaba Trump, "ba zan iya saka wani takunkumi a fuskata ba, ba zan iya karbar manyan baki har mu gaisa ba a yayin da fuskata ke rufe ba."
Trump ya bayyana cewa ba dole bane sai mutum ya bi shawarar da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta bayar ba a kan amfani da takunkumin fuska.
"Ba dole bane sai mutum ya saka, bana jin cewa zai iya saka wani takunkumi a fuskata," a cewar Trump.
Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta tabbatar da cewa mutane 278,458 sun kamu da kwayar cutar covid-19 a kasar sannan cutar ta hallaka mutum 7000, a cewar kididdigar jami'ar 'Johns Hopkins'.
New York ce jihar da ta fi fuskantar barazana daga cutar covid-19 a kasar Amurka, kuma tuni gwamnan jihar, Andrew Cuomo, ya fara neman taimakon sauran sassan kasar Amurka bayan cutar ta kashe mutane kusan 3000 a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng