Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da mutuwar wani mai coronavirus a jahar

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da mutuwar wani mai coronavirus a jahar

- Gwamnatin jahar Lagas ta sanar da mutuwar wani mutum dan shekara 36 sakamakon Coronavirus a jahar

- Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayar da sanarwar ya shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 5 ya watan Afrilu

- Mutumin shine na biyu da ya mutu sakamakon cutar a jahar

Gwamnatin jahar Lagas ta sanar da cewar wani mutum dan shekara 36 ya mutu sakamakon Coronavirus a jahar.

Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayar da sanarwar ya shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 5 ya watan Afrilu.

Ya bayyana cewa dan Najeriyan ya mutu a ranar Asabar a wata cibiyar lafiya mai zaman kanta.

Abayomi ya tabbatar da mutuwar a matsayin na biyu da faru sanadiyar Coronavirus a Lagas.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da mutuwar wani mai coronavirus a jahar

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Lagas ta tabbatar da mutuwar wani mai coronavirus a jahar
Source: Twitter

Ku tuna cewa a ranar Juma’a, 2 ga watan Afrilu ne jaridar Punch ta ruwaito cewa Wani mutum dan shekara 55 ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas, Idi-Araba, wanda shine mutum na farko da ya mutu a Lagas.

Kwamishinan lafiyar, wanda ya tabbatar da cewar Lagas ta sake samun mutane shida da suka kamu da COVID-19, ya ce an dauke wani mara lafiya daga jahar.

Hakan na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan cibiyar hana yaduwar cututtuka na Najeriya (NCDC) ta sanar da cewar an sake samun wanda ya mutu sannan an sallami mutane biyu a ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: An sake samun wanda ya mutu a Najeriya, sun zama mutum 5

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Neja ta janye dokar ta baci da ta sanya a jihar inda aka haramtawa mutane zirga-zirga saboda tsoron yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

A yanzu, an amince mutane su fita harkokinsu daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.

Sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin kar ta kwanan yakin Coronavirus, Ahmed Ibrahim Matane, ya sanar da hakan ne a Minna, yayin hira da manema labarai kan matakan da gwamnatin ke dauka wajen dakile cutar.

Ya ce za'a bude kasuwanni daga karfe 8 zuwa biyu kuma ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki amma zasu tashi karfe 2.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel