An kubutar da mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali da ake wa mutane ukuba

An kubutar da mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali da ake wa mutane ukuba

A ranar Asabar ne jami'an gwamnatin jihar Zamafara suka bayyana cewar sun kubutar da wasu kanjamammun mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali a Gusau.

Akwai alamun firgici da dimaucewa a tattare da mutanen, wadanda yunwa ta bayyana kuru-kuru a jikinsu.

Kwamishinan aiyuka na musamman a jihar Zamfara, Alhaji Mohammed Saddiq Maiturare, ne ya jagoranci jami'an tsaro zuwa gidan bayan bisa umarnin gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Gwamnan ya bayar da umarnin a kai samae irin wadannan haramtattun gidajen gyaran hali a fadin jihar bayan samun cikakken rahoto a kan yadda suke gallazawa mutanen da aka kai musu.

Tawagar jami'an gwamnatin ta samu mutanen da aka killace a gidan, maza da mata, a daure da ankwa a dakunan tabo a gidan da ke karkashin wani mai suna Malam Iliyasu Abdullahi Gamagiwa.

An kubutar da mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali da ake wa mutane ukuba

An kubutar da mutane 54 daga wani haramtaccen gidan gyaran hali da ake wa mutane ukuba
Source: Twitter

Mutanen suna cikin yanayi mai ban tausayi, sannan an same su cikin matsananciyar kishin ruwa.

Mai haramtaccen gidan, Malam Gamagiwa, ya bayyana cewar gidan ya shafe shekaru masu yawa yana aiki. Kazalika, ya bayyana cewa iyaye ne dan kansu suke kawo 'ya'yansu.

DUBA WANNAN: Ku gafarci azarbabina da gazawata: Zulum ya nemi afuwar jama'ar jihar Borno

"Duk wanda ka gani a nan baligi ne da ya zama kangararre ko kuma ya fandare.

"Wasu daga cikinsu barayi ne, wasu suna shan miyagun kwayoyi, akwai wadanda ma dukan iyayensu suke yi. Mu aikinmu shine mu ladabtar da su," a cewarsa.

Sai dai, tuni gwamna Matawalle ya bayar da umarnin a rufe gidan, sannan a gurfanar da masu ita da masu hannu a gudanar da al'amuran gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel