Coronavirus: An sake samun wanda ya mutu a Najeriya, sun zama mutum 5

Coronavirus: An sake samun wanda ya mutu a Najeriya, sun zama mutum 5

- Cibiyar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce an sake samun wanda ya mutu a kasar sakamakon annobar COVID-19

- Hukumar ta sanar da labarin mara dadi a safiyar ranar Lahadi, 5 ga watan Afrilu a shafin twitter yayinda ta tabbatar da samun Karin muten 10 da ke da cutar

- Sai dai hukumar ta NCDC, bata samar da cikakken bayani game da wanda ya mutum ba kamar irin jinsi, jaha ko kuma lokacin da mai shi ya mutu

Adadin wadanda suka mutu a Najeriya sakamakon annobar coronavirus ya karu zuwa 5, a bisa ga bayanin da Cibiyar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta fitar.

Hukumar, a wasu mabanbantan rubutu biyu da ta wallafa a shafin twitter, ta tabbatar da cewar wadanda suka mutu sun kasance mutum 4 a ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu amma sun karu zuwa 5 a ranar Lahadi, 5 ga watan Afrilu.

Sai dai, hukumar NCDC bata riga ta bayar da cikakken bayani kan mutuwar baya-bayan nan ba kamar irin jinsi, jaha ko kuma lokacin da mai shi ya mutu.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya 3 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka

A baya mun ji cewa cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma (10) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 8 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Edo.“

“Kawo karfe 1:15 na ranar 5 ga Afrilu, mutane 224 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 27 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Lagos- 115, Abuja- 45, Osun- 20, Oyo- 9, Akwa Ibom- 5, Ogun- 4, Edo- 9, Kaduna- 4, Bauchi- 6, Enugu- 2, Ekiti- 2, Rivers-1, Benue- 1, Ondo- 1.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel