FG ta yafewa wasu kamfanoni 25 biyan haraji na tsawon shekara uku

FG ta yafewa wasu kamfanoni 25 biyan haraji na tsawon shekara uku

Gwamnatin tarayya ta yafewa kamfanoni 25 kudin haraji karkashin hukumar habaka kudin shiga ta haraji na kamfanoni.

Wannan lamarin kuwa kyautatawa ce daga gwamnatin tarayyar wacce ta ce kada su biya harajin.

Wannan kyautatawar ana kiranta da "hutun haraji" kuma ana yin hakan ne don karfafa guiwar masu saka hannayen jari a cikin tattalin arzikin kasa.

Wannan na nufin kamfanonin ba sai sun biya haraji ba na tsawon wani lokaci. Haka kuwa zai basu damar kafuwa da kara karfi.

Kamfanonin da ake ba irin wannan garabasar sun hada da irin kamfanonin da babu irinsu a kasar nan tuntuni.

Wani kiyasin da aka yi a kan irin kyautatawar nan a 2019 wanda NIPC ta fitar ya nuna cewa an ba kamfanoni 25 irin wannan hutun harajin.

FG ta yafewa wasu kamfanoni 25 biyan haraji na tsawon shekara uku
Hedikwatar hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS)
Asali: UGC

Kamfanonin da suka samu wannan garabasar sune: Royal Mills and Foods Limited, UVA Limited, Pinnacles Apartments Development Limited, Obu Cement Company Limited, Saba Steel Industries Nigeria Limited, Gowus Nigeria Limited, Fidson Healthc4 Plc, Gowus Nigeria Limited, Lafarge Africa Plc, Edimara Properties Limited da Wacot Rice Limited.

DUBA WANNAN: Covid-19: Sauyawar sakamakon gwaji a UBTH ya jefa tsoro a zukatan ma'aikata da jama'a

Sauran sun hada da Aqua Africa Limited, Grand Pela Hotels, Globus Resources Limited, Karshi Agro Farms Limited, Crown Flour Mills Limited, Dharul Fertilizer Limited, Olam Hatcheries Limited, Harvestfield Industries Limited da Jabi Mall Development Company Limited.

Ragowar sun hada da Power Gas Global Investment Limited, Polar Petrochemicals Limited, Montego Upstream Services Limited, Dangote Sinotrucks West Africa da Hayat Nigeria Limited.

Babban sakataren NIPC, Yewande Sadiku, ta ce gwamnati ta mayar da hankali wajen jawo sabbin hannayen jari don habaka tattalin arzikin kasar nan.

Ta ce hukumar ta shiga jerin hadin guiwa daban-daban da wasu bangarori masu zaman kansu wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel