Yan Najeriya 3 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka

Yan Najeriya 3 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka

Benaoyagha Okoyen, karamin jakadan Najeriya a Birtaniya, ya tabbatar da mutuwar yan Najeriya uku wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a kasar Amurka.

A bisa ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) Okoyen ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki.

Wadanda suka mutun sun hada da wani likita daga Abia, Bassey Offiong mai shekara 25 da kuma wata yar shekara 60.

Yan Najeriya 3 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka
Yan Najeriya 3 sun mutu sakamakon COVID-19 a Amurka
Asali: UGC

“Mutum na farko ta kasance Hajia Laila Abubakar Ali mai shekara 60 daga Kano, wacce ta rasu a ranar 25 ga watan Maris yayinda ta ke samun kulawar likita a asibitin Lincoln da ke Bronx, New York.

"Na biyun, Bassey Offiong mai shekara 25 daga Calabar, dalibin ajin karshe da ke karantar Injiniya a jami’ar Western Michigan, Kalamazoo, ya rasu a ranar Asabar, 28 ga watan Maris, a asibitin Beaumont da ke Royal Oak.

"Sai na karshen ya kasance likita, Dr Celeb Anya, daga Ohafia a jahar Abia,” in ji sanarwar.

“Ya rasu yayinda ya ke yiwa al’umma hidima a wajen yaki da annobar COVID-19 a New York a ranar 1 ga watan Afrilu.

“A madadin jakadan Najeriya a New York, Ina mika ta’aziyya ya iyalan yan Najeriyar da suka mutu a mummunan lamarin.”

Ya kuma yaba ma ayyukan likitocin Najeriya a USA da suka yi kokari yaki da hana yaduwar cutar Coronavirus.

KU KARANTA KUMA: Saba dokar hana fita: Jami'an tsaro sun damke motoci 51, babura 46 a Abuja

A wani rahoton mun ji cewa, Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma (10) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 8 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Edo.

“Kawo karfe 1:15 na ranar 5 ga Afrilu, mutane 224 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 27 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel