A fito da sunayen wadanda aka ba kyautar N20, 000 – Sanata Shehu Sani

A fito da sunayen wadanda aka ba kyautar N20, 000 – Sanata Shehu Sani

Ku na da labari cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa za ta kawowa mutane miliyan 11 dauki a fadin kasar nan domin rage masu radadin da ake fama da shi a halin yanzu.

A dalilin wannan ne Ministar bada agaji da tallafin Najeriya, Sadiya Umar Farouk ta ke jagorantar rabon kudin da ake yi wa marasa karfi a Najeriya, inda ake rabawa wasu N20, 000.

Kwamred Shehu Sani ya fito ya kalubalanci wannan shiri a kaikaice kamar yadda mu ka samu labari. Shehu Sani ya yi wannan magana ne ta dandalin sada zumuntansa na Tuwita.

Tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya fito shafinsa na Tuwita ya na cewa gwamnatin tarayya ta fito da sunaye da cikakken bayani game da wadanda su ka amfana da wannan kudi.

Sani ya rubuta: “A fito a wallafa sunaye da cikakken bayanin wadanda aka ba kyautar N20, 000.” Bisa dukkan alamu Sani ya na wannan magana ne da gwamnatin shugaban Buhari.

KU KARANTA: Ba zan garkame fuska ta da wata tsumma ba - Trump

Wannan magana da ‘Dan siyasar ya yi ta jawo surutai a kafar sada zumuntar. A daidai lokacin da wasu su ke yabonsa na kiran ayi ke-ke-fda-ke-ke, wasu kuma sun fito su na sukarsa.

Wani Mutumi mai suna Muhammad ya bayyana cewa babu bukatar a taso gwamnati a gaba a kan cewa sai ta wallafa sunayen wanda ta ba rabawa wannan N20, 000 a wasu jihohi.

A cewar wannan Mutumi, Sani bai yi kokarin ganin an yi irin wannan gaskiya-da-gaskiya a gwamnati a lokacin da aka zabe shi zuwa majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019 ba.

Shi kuma wani Mai suna Eliotigbe a Tuwita, cewa ya yi gwamnatin tarayya karya kawai ta shararawa jama’a da ikirarin da ta yi na rabawa wasu Marasa karfi biliyoyin kudi.

Wani Bawan Allah kuma ya koka ne game yadda jama’a ba su yarda da abin da gwamnati ta fada. Afolabi Abiola Yusuf fitowa ya yi, ya na cewa duk wanda ya yi karya, zai iya tafka sata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel