Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa

Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa

A ranar Asabar ne shugaban kasar Amurka, Donad Trump, ya bayyana cewa ba zai iya rufe fuska da takunkumi ba duk da sabuwar dokar kare lafiya a kasar Amurka ta bawa 'yan kasar shawarar amfani da takunkumin domin kare kansu daga kamuwa da kwayar cutar covid-19.

A cewar shugaba Trump, "ba zan iya saka wani takunkumi a fuskata ba, ba zan iya karbar manyan baki har mu gaisa ba a yayin da fuskata ke rufe ba."

Trump ya bayyana cewa ba dole bane sai mutum ya bi shawarar da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta bayar ba a kan amfani da takunkumin fuska.

"Ba dole bane sai mutum ya saka, bana jin cewa zai iya saka wani takunkumi a fuskata," a cewar Trump.

Ba zan rufe fuskata da takunkumi ba - Trump ya bayyana dalilansa
Donald Trump
Asali: Getty Images

Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta tabbatar da cewa mutane 278,458 sun kamu da kwayar cutar covid-19 a kasar sannan cutar ta hallaka mutum 7000, a cewar kididdigar jami'ar 'Johns Hopkins'.

DUBA WANNAN: Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya

New York ce jihar da ta fi fuskantar barazana daga cutar covid-19 a kasar Amurka, kuma tuni gwamnan jihar, Andrew Cuomo, ya fara neman taimakon sauran sassan kasar Amurka bayan cutar ta kashe mutane kusan 3000 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel