Gwamnatin Tarayya ta na so ta warewa annobar Coronavirus N500bn - Ahmed
A yayin da Duniya ta shiga cikin annoba, gwamnatin tarayya ta kawo shawarar kafa wani asusu na musamman da za ayi amfani da shi wajen kawo karshen cutar COVID-19 a Najeriya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta na neman amincewar majalisar tarayya wajen kafa wannan asusun tallafi. Daily Trust ta rahoto cewa gwamnati ta na neman tara kudi Naira biliyan 500.
Ministar tattalin arziki da tsare-tsare da kasafin kudin Najeriya, Zainab Ahmed Shamsuna ta bayyana wannan a wajen wani taro da ta yi da shugabannin majalisar wakilai da dattawa.
A wajen wannan zama da aka yi Ranar Juma’a Misis Zainab Ahmed Shamsuna ta yi wa ‘Yan majalisar bayanin yadda za a nemo wannan makudan kudi da kuma yadda za a batar da su.
A cewar Ministar wannan asusun tallafi zai samu gudumuwa ne daga wasu kudi na musamman da ake warewa Najeriya game da kuma aro daga manyan hukumomin da ake da su a Duniya.
KU KARANTA: An fara gina babban wurin ajiye gawa a Landan saboda annobar COVID-19
Zainab Ahmed ta bayyana cewa za a ayi amfani da wadannan kudi wajen bunkasa asibitocin kasar nan. Bayan haka gwamnatin tarayya za ta yi amfani da kudin wajen kawowa jihohi dauki.
Shugaban majalisar Najeriya Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila sun halarci wannan taro. Mataimakansu, Ovie Omo-Agege da Idris Wase duk sun samu zama da Ministar kudin.
Ahmed ta shaidawa ‘Yan majalisar cewa: “Gwamnatin tarayya ta na bukatar ta zama za ta iya inganta kayan aikin kiwon lafiya a jihohin Najeriya, sannan kuma ta kawowa jihohi tallafi.”
Haka zalika Ahmed ta shaidawa ‘Yan majalisar cewa wannan kudi za su yi amfani wajen tallafawa tsare-tsaren gwamnatin tarayya da ke karkashin hukumar NDE mai samar da aikin yi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng