Tallafin Coronavirus: An kama shugaban APC yana amsan lambobin asusun bankunan jama’a

Tallafin Coronavirus: An kama shugaban APC yana amsan lambobin asusun bankunan jama’a

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo ta sanar da kama wani shugaban jam’iyyar APC a matakin mazaba a jahar Edo, Mista Sunday Erhabor da yunkurin damfarar jama’a da sunan basu tallafin gwamnati.

Daily Trust ta ruwaito Yansandan sun kama Sunday ne yayin da yake karbar bayanan asusun bankunan jama’a tare da sunayensu da sunan wai sama musu tallafin da gwamnati ta tanada domin rage ma jama’a radadin mawuyacin halin da aka shiga sakamakon bullar annobar Coronavirus.

KU KARANTA: Hukumar NCDC ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta daga masu cutar Corona

Tallafin Coronavirus: An kama shugaban APC yana amsan lambobin asusun bankunan jama’a
Tallafin Coronavirus: An kama shugaban APC yana amsan lambobin asusun bankunan jama’a
Source: Twitter

Da wannan shiri na gwamnati ne Sunday ya fake yana bin jama’a yana amsan bayanan bankunansu, inda yake ikirarin cewa gwamnatin jahar ce ta sanya shi gudanar da wannan aiki, kuma a madadin shuwagabannin jam’iyyar na matakin karamar hukumar yake wannan aiki.

Sai dai mai magana da yawun gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki, watau Mista Crusoe Osagie ya musanta ikirar Sunday, inda yace da farko ma dai ai gwamnati ba jam’iyya bace.

“Kayan tallafin da gwamnatin Gwamna Godwin Obaseki ta sayo ta tanadesu ne domin amfanin talakawa gajiyayyu, kuma nan bada jimawa ba zamu wallafa karin bayani game da shirin rabon tallafin.

“Don haka nake shaida ma jama’a da su kula, saboda gwamnati bata dauki wani mutumi ko wata kungiya aikin tattara sunaye da bayanan asusun bankunansu ba, don haka jama’a su yi watsi da irin wannan bayanan.” Inji shi.

A wani labari kuma, wani dan majalisar dokokin jahar Bauchi dake wakiltar al’ummar mazabar Bagoro, Musa Nakwada ya bayyana albashinsa a matsayin dan majalisa, sa’annan ya sadaukar da makudan kudin domin ganin an yaki annobar Coronavirus a jahar.

Daily Trust ta ruwaito dan majalisa Musa Nakwada ya bayyana cewa ya bayar da kafatanin albashin na N476,000 ga kwamitin ko-ta-kwana da gwamnatin jahar Bauchi ta samar domin yaki da cutar Coronavirus, watau COVID-19.

A cewarsa, ya yi haka ne domin taimaka ma wannan kwamiti domin gudanar da aikinta na kare yaduwar cutar a jahar, wanda ta tilasta ma gwamnan jahar, Sanata Bala Muhammad killace kansa bayan ya kamu da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel