Babban magana: An nemi a kacaccala masarautar Minna zuwa yanka 5

Babban magana: An nemi a kacaccala masarautar Minna zuwa yanka 5

- Wata kungiya a masarautar Minna ta nemi a kacaccala masarautar zuwa yanka biyar

- Kungiyar a wata wasika da ta aike wa kakakin majalisar dokokin jahar Niger, ta nemi a samar da masarautun Kuta, Paiko, Galadiman Kogo, Bosso/Minna da kuma na Kafin Koro

- Hakan ya biyo bayan wasu nade-nade na hakimai da sarkin Minna ya yi wanda suke ganin babu adalci a ciki

Wata kungiya ta al’umma a masarautar Minna, ta yi kira ga raba masarautar zuwa gidaje biyar.

Kungiyar a wata wasika da ta aike wa kakakin majalisar dokokin jahar Niger, ta nemi a samar da masarautun Kuta, Paiko, Galadiman Kogo, Bosso/Minna da kuma na Kafin Koro.

Wasikar na dauke da sa hannun wakilai daga dukkanin yankuna guda shida da suka kafa masarautar Minna.

Babban magana: An nemi a kacaccala masarautar Minna zuwa yanka 5

Babban magana: An nemi a kacaccala masarautar Minna zuwa yanka 5
Source: Twitter

Sun bayyana cewa sun yi wannan kira ne saboda kin aiwatar da rahoton kwamitin da gwamnatin jahar ta kafa domin duba cikin zargin nade-naden hakimai ba bisa ka’ida ba da sarkin Minna ya yi.

Sun tuna cewa an kafa kwamitin ne biyo baya nade-naden wasu hakimai biyu da aka yi daga bangare guda.

Sun tuna cewa kwamitin ya bayar da shawarar nada hakimai bakwai ta yadda za a samu biyar daga kowani bangare sannan biyu daga masarautar Bosso/Minna, wanda gaba daya suka kafa masarautar.

Sun jadadda cewar idan dai ba za a aiwatar da hakan ba, toh lallai dole a kacaccala masarautar zuwa yanka-yanka.

Yayinda suke yaba ma gwamnan kan abunda suka bayyana a matsayin adalcinsa da son ganin tarihin masarautar ya ci gaba ba tare da wargajewa ba, masu korafin sun ce kokarin da wasu dattawa suka yi domin ganin an magance matsalar bai cimma nasara ba.

Sakatariyar majalisar masarautar bata yi martani kan korafin ba.

A halin da ake ciki, babban sakatariyar labaran gwamnan, Misis Mary Noel Berje, da aka tuntube ta, tace bata da masaniya kan korafin.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Soja ya kashe wani mutum bayan an sanya dokar hana fita saboda coronavirus a Delta

A wani rahoton kuma, mun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nemi afuwar mutanen jihar Borno a kan raunin da yake da shi da kuma gazawarsa yayin da yake jagorantar gwamnatin jihar.

A ranar Talata ne Zulum ya rufe wasu gidajen sayar da man fetur guda 10 da ke Maiduguri bayan samunsu da laifin boye man fetur.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wasu gidajen sayar da man fetur a jihar Borno sun boye mai tare da sayar da shi a farashi mai tsada tun bayan sanarwar matakan dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Hakan ne yasa gwamna Zulum da kansa ya kai wata ziyarar bazata a irin gidajen man da ake zargi da aikata hakan domin tilasta su budewa tare da sayarwa da jama'a man a kan farashin da gwamnati ta yanke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel