Wata sabuwa: Soja ya kashe wani mutum bayan an sanya dokar hana fita saboda coronavirus a Delta
Rundunar yan sanda a jahar Delta ta bayyana cewa wani jami’in soja da ba a san ko wanene ba ya harbi wani matashi har lahira a jahar, Channels TV ta ruwaito.
Lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a garin Ugbuwangue da ke karamar hukumar Warri ta Kudu a jahar, a rana na biyu da fara aikin dokar hana fita wanda gwamnan jahar, Ifeanyi Okowa ya sanya.
Hukumar yan sanda a jahar ta tabbatar da kisan, inda ta bayyana cewa ta fara bincike a lamarin.
Jami’ar hulda da jama’a na yan sanda a jahar, Onome Onovwakpoyeya, ta bayyana cewa basu samu cikakken bayani kan lamarin ba.
Ta ce: “Eh da gaske ne. Ya faru ne a yau, kamar yadda aka sanar dani, amma babu cikakken bayani tukuna.”
Shugaban karamar hukumar Warri ta Kudu, Mista Michel Tidi, ya bayyana cewa ya sanar da hukumomin da ya kamata batun.
Ya yi bayanin cewa ya halarci wani taro da aka gudanar a ofishin kwamandan yan sanda a Warri, kan lamarin.
A cewar Tidi, wakilan rundunar yan sanda da na sauran hukumomin tsaro, da Shugaban garin da jagoran ahlin wanda aka kashe duk sun hallara.
A kan abunda aka tattauna a taron, ya bayyana cewa sun bukaci cewa a hukunta dojan yayinda aka ba da tabbacin cewa za a yi adalci.
A wani rahoto na daban, mun ji cewa Cibiyar kiyaye yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta tabbatar da sabbin mutane 10 da suka kamu da kwayar cutar wanda hakan ke nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 184.
Hukumar ta NCDC a shafin ta na Twitter a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu ta bayyana cewa an samu sabbin mutane 7 da suka kamu da cutar a Legas yayin da aka samu wasu uku a Abuja.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa Gwamna Sanwo-Olu ya fito
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng