Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya
Gwamnatin jihar Kano ta bude shafin yanar gizo domin fara rijistar masu shawa'ar zama 'yan agaji a bangaren kiwon lafiya domin taimakawa jihar a yakin da take yi da yaduwar annobar cutar covid-19.
Jami'ar hulda da jama'a a ma'aikatat lafiya ta jihar Kano, Hadiza Namadi, ce ta fadi hakan ranar Alhamis a cikin wani sako da ta aikwa manema labarai.
Hadiza ta bayyana cewa gwamnati ta gayyaci wadanda suka nemi aikin domin tantancewa, wacce aka fara ranar Laraba, amma aka dakatar saboda yawan masu neman aikin da suka cushe wurin tantancewar..
"A kokarin gwamnati na shawo kan cunkuson masu sha'awar aikin, shine a bude shafin yanar gizo domin takaita wa masu sha'awar aikin wahala," a cewar saanarwar.
Ma'aikatan lafiyar 'na sa ka' da ake nema sun hada likitoci, ma'aikatan kula da lafiyar al'umma, masu karatun taimakon likitoci a asibiti da sauran kwararru a bangaren aikin lafiya.
DUBA WANNAN: Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19
Sauran ragowar ma'aikatan lafiyar da ake nemaa sun hada da masu kimiyyar gwaje-gwaje a asibiti, masana kimiyyar magunguna, malaman tsafta da sauransu..
Ana bukatare masu sha'awar agajin su kasance mazauna Kano.
Shafin neman aikin shine kamar haka: www.kanostate.gov.ng/volunteers.
Jihar Kano na daga cikin jihohin sa suka kasance a sahun gaba wajen saka dokar rufe iyakoki, kasuwanni da hana walwalar jama'a saboda barazanar annobar covid-19
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng