Coronavirus: 'Yar shugaba Buhari ta kammala killace kanta lafiya

Coronavirus: 'Yar shugaba Buhari ta kammala killace kanta lafiya

Labari da muke samu ya nuna cewa ‘yar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta dawo daga kasar Birtaniya makonni da suka gabata ta kammala killace kanta na tsawon makonni biyu, kamar yadda cibiyar lafiya ta ba da shawara ga wadanda suka dawo daga kasashen waje a kwanan nan.

Hakan na daga cikin kokarin da gwamnatin tarayyar kasar ke yi na ganin ta hana yaduwar cutar coronavirus wacce ta addabi kasashen duniya.

Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ce ta sanar da fitowar ‘yar tata yayinda ta ke nuna farin ciki kan haka bayan ta shafe tsawon makonni biyu ba tare da ta hada ido da ‘yar tata ba.

Ta kuma yiwa wadanda suka kamu da cutar fatan alkhairi da samun lafiya, da fatan Allah ya kawo karshen annobar.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, Aisha ta ce: "abun farin ciki ne na sake yin ido biyu da diyata bayan kwashe mako biyu a killace. Ina yi wa duk masu cutar fatan waraka sannan ina fatan Allah zai kawo karshen wannan annoba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan daya

A wani labarin kuma, mun ji cewa Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun sauki sosai amma likitocinsa sun nemi ya kara hutawa sosai kamar yadda wasu majiyoyi na kusa dashi suka bayyana, jaridar The Cable ta ruwaito.

Na hannun damar Shugaban kasar ya kamu da cutar Coronavirus a makon da ya gabata amma ya fuskanci alamun ciwon kadan-kadan ne, in ji majiyoyi daga gidansa.

“Tun bayan da ya kwanta, yana dan tari lokaci zuwa lokaci, wanda ya ci gaba koda dai bai jigata shi ba, don haka ya yanke shawarar komawa asibiti mai zaman kansa a Lagas domin cigaba da gwaje-gwaje da kuma kula da yanayin ciwon,” cewar majiyar a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu.

“Har zuwa yanzu, baya jin zazzabi mai zafi kan wahala wajen numfashi, kuma tarin ya fara sauki bayan kulawar likita da yake samu, don haka akwai ci gaba sosai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel