UK: Yawan mutanen da COVID-19 ta ke kashewa ya sa ana gina dakin ajiye gawa

UK: Yawan mutanen da COVID-19 ta ke kashewa ya sa ana gina dakin ajiye gawa

Kawo yanzu, cutar nan ta Coronavirus ta ratsa kasahe fiye da 190 a Duniya, inda ta hallaka fiye da mutum 50, 000 daga karshen shekarar bara zuwa yanzu.

Ba a bar Kasar Ingila a baya wajen ta’adin wannan annoba ba. A dalilin haka ne dazu mu ka ji cewa gwamnatin Birtaniya ta dauki mataki game da lamarin.

Jaridar Mirror ta kasar Ingila ta fitar da rahoto cewa ana gina wasu manyan dakunan ajiye gawa. Ana wannan aiki ne saboda yawan mutuwar da ake yi a kasar.

Wadannan dakuna da ake ginawa a Yankin Wanstead a tashar Manor da ke kusa da babban birnin Landan sun kai girman filayen wasan kwallon kafa biyu.

Daidai kusa da wannan gini da ake yi, akwai dakunan jinyar da asibitin NHS Nightingale su ke ginawa. Wannan aiki zai ci kimanin gadajen marasa lafiya 4000.

KU KARANTA: Gwamnoni sun yi taron NEC da Osinbajo ba tare da an zauna a ofis ba

UK: Yawan mutanen da COVID-19 ta ke kashewa ya sa ana gina dakin ajiye gawa
COVID-19 ta kashe Likitan Najeriya Alfa Saidu da dubunnai a Ingila
Asali: Twitter

Hakan na nufin duk wanda ya kwanta dama a sanadiyyar COVID-19 a wannan asibiti na Nightingale, za a dauke shi zuwa wurin ajiye gawan da aka tanada a gefe.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran za a kammala wannan aiki cikin ‘yan makonni masu zuwa. Ba a bayyana ainihin lokacin da ake tunanin wurin zai soma aiki ba.

Mazauna wannan Yanki sun samu labarin wannan katafaren gini. Shugaban Gundumar Newham, Mista Rokhsana Fiaz, shi ne ya aikowa Mazauna wurin takarda.

Rokhsana Fiaz ya sanar da mutanen Birnin Newham cewa za a gina wannan wuri domin a rika adana gawa ne ganin irin mace-macen da ake samu yanzu a cikin Birtaniya.

Dazu kun ji labari cewa ‘Dan wasan damben nan na kasar Birtaniya, Anthony Joshua ya fito ya na kokawa game da yadda cutar COVID-19 ta ke ta raba shi da na-kusa da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng