Coronavirus: Sakamakon gwajin mutane 22 cikin 25 da ake zargin sun kamu a Kano ya fito

Coronavirus: Sakamakon gwajin mutane 22 cikin 25 da ake zargin sun kamu a Kano ya fito

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin Jahar kano na gudanar da bincike a kan wasu mutane 25 da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a jahar.

A wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a Kano, Kwamishinan Lafiya a Jahar, Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana tuni gwaji ya nuna 22 daga cikinsu ba sa dauke da cutar yayin da ake jiran sakamakon gwaji na mutum uku.

Kwamishinan ya kara da cewa mafi yawan rahotannin da suke samu daga mutane, jita-jita ce, sannan ya ce sun samar da wasu lambobi na kira domin bayar da rahotannin wadanda ake tunanin sun kamu da cutar.

Coronavirus: Sakamakon gwajin mutane 22 cikin 25 da ake zargin sun kamu a Kano ya fito
Coronavirus: Sakamakon gwajin mutane 22 cikin 25 da ake zargin sun kamu a Kano ya fito
Asali: UGC

Har ila yau a wani rubutu da hadimin shugaba kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter ya jadadda jawabin Tsanwa a kan batun.

Ya ce: “22 daga cikin 25 da ake zargin suna dauke COVID19 a jahar Kao basa dauke da ita kamar yadda gwaji ya nuna, sannan ana jiran sakamakon gwajin sauran mutum uku, kwamishinan lafiya na jahar, Dr Aminu Tsanyaa ya bayyana a yau.”

Har ila yau mun ji cewa Aminu Ibrahim ya ce Alhaji Aliko Dangote zai gina cibiyar kebe masu coronavirus mai gado 500, sabanin 600 da wasu kafofin yada labarai suka rawaito.

Kwamishinan ya kuma jaddada kokarin gwamnatin Kano na ci gaba da sanya ido kan dokar hana shiga jihar da suka kafa tun a makon da ya gabata.

Makociyarta wato Jihar Kaduna, dokar hana fita baki daya aka saka duk da cewa gwamnati ta sassauta a ranar Laraba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Sakamakon gwajin da aka yiwa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da uwargidarsa, Hafsat Ganduje ya nuna basa dauke da cutar coronavirus.

Abba Anwar, babban sakataren labaran gwamnan ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a Kano.

Ya bukaci jama’a da su lazumci wanke hannayensu a ruwa mai kwaranya da sabulu ko abun kasha kwayoyin cuta, tsaftar muhalli da kuma nisantan taron jama’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel