Coronavirus: Kasar Saudiyya ta saka dokar ta baci a Makkah da Madinah
A yau, Alhamis, ne gwamnatin kasar Saudiyya ta saka dokar ta baci ta sa'a 24 a birnin Makkah da Madinah a matsayin kara tsaurin matakan dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus da ta kama mutane 1,700 tare da kashe mutane 16.
A sanarwar da ta fiito daga ofishin ministan harkokin cikin gida na Saudiyya, gwamnatin kasar za yi wasu muhimman ma'aikata da 'yan kasuwa uzuri domin bawa jama'a damar sayen kayan abinci da magani.
Motocin haya a biranen za suke daukan fasinja daya ne jal domin tabbatar da jama'a sun nesanta da junansu ta yadda kwayar cutar ba zata cigaba da yaduwa ba, a cewar sanarwar.
Kasar Saudiyya, mai yawan mutane miliyan 30, ta dauki tsauraran matakai da suka hana da hana saukan jirage, rufe yawancin wuraren haduwar mutane tare da dakatar da aikin Umrah duk domin shawo kan annobar kwayar cutar covid-19.
A ranar Talata ne hukumar kasar Saudiyya ta umarci kasashen duniya su dakatar a karbar kudin maniyyata aikin Hajjjin bana da ake saka ran gudanar wa a cikin shekarar nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanar wa da ma'aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudi Arabia ta fitar a ranar Talata, 31 ga watan Maris.
DUBA WANNAN: Sakon faifan bidiyon masu dauke da covid-19 ga sauran 'yan Najeriya
A cikin sanarwar da ministan ma'aikatar ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce za a dakatar da karbar kudin maniyyatan ne har zuwa lokacin da al'amura za su koma daidai.
A cewar sanarwar, ba za a yi gaggawar yanke hukunci a kan aikin Hajjin bana ba har sai an ga yadda abubuwa zasu je su dawo dangane da barkewar annobar cutar coronavirus a fadin duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng