Coronavirus: Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci gwamnatoci su ba talakawa abinci

Coronavirus: Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci gwamnatoci su ba talakawa abinci

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban cibiyar lafiya ta duniya wacce aka fi sani da WHO, Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira ga gwamnatoci da su bai wa talakawa abinci domin rage kunar zuciya da suke ciki sakamakon hana su fita daga gidajensu.

Idan dai za ku tuna kasashe da dama sun dauki matakai da dama ciki harda tursasa mutane zaman gida a kokarin hana yaduwar cutar covid-19 wacce aka fi sani da coronavirus.

Wannan dalili ne ya sa yawancin talakawa suke kokawa kan matakin saboda wasu sai sun fita suke samun abun sanya wa a baki a kullun, sai dai dama gwamnatoci da yawa sun bullo da tsarin bai wa marasa galihu abinci

Coronavirus: Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci gwamnatoci su ba talakawa abinci
Coronavirus: Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci gwamnatoci su ba talakawa abinci
Asali: Depositphotos

A wani rubutu da Mista Ghebreyesus ya wallafa a Twitter a ranar Alhamis, ya ce ko da yake rufe kasashe da hana mutane fita daga gidajensu yana iya rage yaduwar cutar ta covid-19, wadannan matakai za su iya yin mummunar illa ga talakawa da marasa galihu.

"Ina kira ga kasashe su tabbatar cewa wadannan mutane wato talakawa da marasa galihu sun samu abinci da sauran kayan bukatu a wannan mawuyacin hali," in ji Mista Ghebreyesus.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na kwanaki 14 a jahar

A wani labari kuma, mun ji cewa wata mata musulma daga Jammu da Kashmir ta bada sadakar kudin da ta dinga tarawa don zuwa aikin hajji. Jimillar kudin ya kai Rs. 500,000 don yakar cutar coronavirus.

Khalida Begum mai shekaru 87 ta adana makuden kudaden ne don shirin tafiya aikin hajji da take yi a 2020. Ta kuwa sadaukar da kudin ne don tallafi ga jama'a sakamakon barkewar muguwar cutar coronavirus. Sakamakon rufe kasar Saudi Arabia da aka yi, ta canza tsarinta inda ta yanke hukuncin bada sadakar dukkan kudin.

Hajji babban al'amari ce a rayuwar kowanne musulmi.

Khalida Begum ta ga jama'a masu yawa na fama ne sakamakon barkewar muguwar cutar a duniya. A don haka ne ta yanke hukuncin sadaukar da tafiya hajjinta don tallafar rayuwar jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel