Gwamnatin Tarayya ta na yi wa COVID-19 kyakkyawar shiri – Yemi Osinbajo

Gwamnatin Tarayya ta na yi wa COVID-19 kyakkyawar shiri – Yemi Osinbajo

A daidai lokacin da ake cigaba da fama da annobar cutar Coronovirus a Duniya, mun samu labari cewa gwamnoni sun gana da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto a Ranar 2 ga Watan Afrilu, Mai girma Yemi Osinbajo ya gana da gwamnonin Najeriya a taron majalisar tattalin arziki na NEC.

Yemi Osinbajo ya shaidawa gwamnonin cewa gwamnatin tarayya ta na shirya wani babban tsarin tattalin arziki da zai taimakawa kasar a wannan lokaci da aka shiga annoba.

Da ya ke magana a jiya Ranar Larana da rana, Mataimakin shugaban na Najeriya, Osibajo ya ce gwamnati ta na kokarin kawo wata hanya da za ta rage radadin da ake ciki a yau.

Mataimakin shugaban kasar ya yi wani zama na musamman ne da kwamitin da majalisar NEC ta kafa domin kawo karshen cutar COVID-19 a jihohin kasar nan da fadin Najeriya.

KU KARANTA: Coronavirus ta sa za a yi wa Majalisa gibin N25b a kasafin kudin 2020

Gwamnatin Tarayya ta na yi wa COVID-19 kyakkyawar shiri – Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo ya yi zama da Gwamnatocin jihohi a kan annobar COVID019
Asali: UGC

Osinbajo ya tabbatarwa gwamnoni cewa gwamnatin tarayya za ta bada gudumuwa ga jihohinsu wajen ganin Bayin Allah sun kubuta daga wannan cuta da ta ke hallaka mutane.

Gwamnonin da su ka halarci wannan taro ta kafar bidiyo sun hada da: Dr. Kayode Fayemi, Nasir El-Rufai, Abdullahi Sule, Mohammed Abubakar Badaru, da kuma David Umahi.

Sauran gwamnonin da su ke cikin wannan kwamiti su ne Dapo Abiodun, da Atiku Bagudu, Kebbi. Ragowar ‘yan kwamitin su ne Ministar kudi da Darektan ofishin kasafin kudi.

Yemi Osinbajo ya ce wannan kwamiti da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar zai rika zama a kowane mako domin ganin inda aka dosa a yaki da cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel