Jam’iyyar APC ta fatattaki dan majalisar tarayya daga jahar Gombe saboda cin amana

Jam’iyyar APC ta fatattaki dan majalisar tarayya daga jahar Gombe saboda cin amana

Jam’iyyar APC reshen mazabar Kumo ta gabas a karamar Akko ta jahar Gombe ya sanar da fatattakar dan majalisa mai wakiltar Akko a majalisar wakilan Najeriya, Usman Bello Akko saboda cin amanar jam’iyya.

Legit.ng ta ruwaito shuwagabannin jam’iyyar sun bayyana haka ne cikin wata wasika da suka aika ma shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Afrilu, 2020, inda suka ce sun dauki matakin ne bayan samun korafe korafe a kan dan majalisar.

KU KARANTA: Boko Haram: Kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da sabbin hare hare

Jam’iyyar APC ta fatattaki dan majalisar tarayya daga jahar Gombe saboda cin amana
Jam’iyyar APC ta fatattaki dan majalisar tarayya daga jahar Gombe saboda cin amana
Asali: Facebook

Shugaban APC na mazabar, Musa Barde ne ya rattafa hannu a kan wasikar tare da wasu jiga jigan jam’iyyar su 20, inda yace sun kafa kwamitin mutane 7 don su bincike korafe korafen da aka yi ma dan majalisar.

“Cewa sanannen lamari ne yadda Usman Bello Kumo ya yi adawa da gwamnan jahar Gombe, Muhammadu Inuwa a yayin zaben gwamnan jahar na 2019, kuma jam’iyya ba za ta lamunci hakan ba domin ya saba ma sashi na 21, sakin layi na A(1) da (2) na kundin dokokin jam’iyyar.

“Cewa Usman Bello Kumo ya bayar da kyautara mota ga wani sojan baka Garba Inuwa Gona wanda ba ma dan mazabar Akko bane, amma kawai saboda ya zagi shugabanmu Muhammad Danjuma Goje a wani shirin gidan rediyon Progress Radio, Gombe.

“Wannan ya nuna rashin da’a, rashin kunya da rashin ganin girman na gaba tare da kin biyayya ga gwamnan jahar Gombe, wanda tabbas zai shafi jam’iyyar mu. Don haka mun sallami Usman Bello Kumo daga jam’iyyar APC ba tare da bata lokaci ba daga ranar 30 ga watan Maris, 2020.” Inji wasikar.

Daga karshe jam’iyyar ta nemi jam’iyyar APC a matakin karamar hukuma da kuma matakin jaha da ta yanke shawarar da take ganin ya dace a kan batun, kuma sanar da uwar jam’iyya ta kasa matakin da ta dauka.

A wani labarin kuma, a wani labari kuma, mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’an jahar Kano su cigaba da bin dukkanin matakan kare kai daga kamuwa da annobar cutar Coronavirus, tare da yin biyayya ga shawarwarin masana kiwon lafiya.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake yi ma al’ummar Kano jawabi a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, inda ya koka tare da bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yawaitan cutar a Najeriya.

Sarki ya ce ya umarci dukkanin hakimansa da dakatai da kuma shuwagabannin addinai su cigaba da sa ido a kan jama’a, kuma su kai rahoton duk inda aka samu wani dake dauke da alamomin cutar da basu gane ba ga masana kiwon lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel