Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration

Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede ya bayyana cewa kamuwa da yayi da cutar Coronavirus ta sa ya zamto mutum mai tawali’u, tare da kaskantara da kan sa.

Punch ta ruwaito Babandede ya bayyana haka ne daga inda aka killace shi a karo ba farko, inda yace sakamakon gwajin da aka masa ne ya nuna yana dauke da cutar bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya a ranar 22 ga watan Maris.

KU KARANTA: Annobar Corona: Ku kama duk wanda kuka ga bai sa kyallen rufe fuska ba – Gwamna ga Yansanda

Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration
Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration
Asali: UGC

Babandede ya nemi yan Najeriya su cigaba da addu’ar Allah Ya kiyaye yaduwar cutar, domin kuwa idan hakan ya faru zata kwashi rayukan jama’a da dama, kwanturolan ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo, inda yace jama’an kauyensu da sauran yan Najeriya suna ta masa addua’r samun sauki.

“Ina mika godiya ta ga abokaina, masoyana, hafsohin hukumar, kananan jami’ai, Musulmai da Kiristocin Najeriya da ma wadanda ke kasashen waje bisa addu’o’in da suka yi min, ina godiya da addu’o’inku, maganan gaskiya ina samun sauki a dalilin addu’o’inku.

“Na gode ma Allah da ya san a kamu da wannan cutar saboda ta bani damar kaskantar da kaina, tare da yin tawali’u, kuma ya bani daman adadin masoyan da nake dasu, a yau 1 ga watan Afrilu na tura wannan bidiyo domin na fada muku ina samun sauki.

“Don Allah ku kula da kanku, ku wanke hannuwanku, kuma ku kauce ma shiga cikin cunkoson jama’a, ku cigaba da yi ma Najeriya adduar kada ta fada cikin mawuyacin hali a dalilin wannan cuta, har yanzu adadin masu ciwon basu yi yawa ba, amma mu cigaba da addu’ar kada adadin ya karu.” Inji shi.

Daga karshe Babandede ya aika sakon soyayyarsa ga jama’an kauyensa, jama’an Kano, Legas, Abuja da duk sauran mutanen da suka nuna masa soyayya tare da ba shi kwarin gwiwa.

Zuwa yanzu dai wannan cuta mai toshe numfashi ta kama mutane 171 a Najeriya tare da kashe mutane 2, jahar Legas da Abuja ne ke da yawancin adadin masu dauke da cutar, kuma a yanzu suna cikin dokar ta baci na sa’o’i 24 domin kare yaduwar cutar a kasar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel