Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na kwanaki 14 a jahar

Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na kwanaki 14 a jahar

Gwamnatin jahar Bauchi ta sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon kwanaki 14 a fadin jahar daga cikin kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus a jahar.

Hakan ya biyo bayan samun karin wani mutum da ya kamu da cutar ta covid-19 a jahar a ranar Talata.

Mutumin da ya kamu da cutar na da shekaru 57 sannan har an aika dashi asibitin koyarwa na Jami’ar Tafawa Balewa domin a ci gaba da kulawa da shi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Bala Mohammed na daya daga cikin mutane uku din da suka kamu da cutar a jahar.

Gwamna Bala Mohammed da ke kwance a asibiti ya Sanar da dokar hana walwala a jahar yana mai cewa dokar zai fara aiki ne ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, da karfe 6:00 na yamma. Sannan cewa za a rufe dukkanin iyakokin jahar.

Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na kwanaki 14 a jahar

Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na kwanaki 14 a jahar
Source: Facebook

Hakazalika domin rage wa mutane wahalan talauci yayin da suke zaman gida za a sassauta dokar a ranar Asabar da Laraba na kowace mako daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma saboda su rika fita domin siyan kayan abinci da kayan da za su bukata.

Duk masu harkoki da ya shafi al’umma ba za su zauna a gida ba.

Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ga wannan mataki da gwamnati ta dauka a matsayin hanyar dakile yaduwar coronavirus a jahar.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon gwaji ya nuna Ganduje da matarsa basa dauke da cutar Covid-19

A wani labari na daban mun ji cwa wasu masallata da adadin su ya dara 25 sun kai wa jami'an kwamitin kar ta kwana na hana yaduwar kwayar cutar Covid-19 na jihar Legas hari a babban masallacin unguwar Agege a yayin da jami'an suka ziyarci masallacin domin tabbatar da cewa mutanen suna bin dokar da gwamnatin jihar ta saka.

A wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Twitter @followlasg, gwamnatin jihar Legas ta yi Allah wadai da halin da matasan suka nuna na saba dokar da jihar ta saka tare da yunkurin kai wa jami'an gwamnati hari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel