Sakamakon gwaji ya nuna Ganduje da matarsa basa dauke da cutar Covid-19

Sakamakon gwaji ya nuna Ganduje da matarsa basa dauke da cutar Covid-19

Sakamakon gwajin da aka yiwa gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da uwargidarsa, Hafsat Ganduje ya nuna basa dauke da cutar coronavirus.

Abba Anwar, babban sakataren labaran gwamnan ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a Kano.

‎“Mun gode Allah madaukakin sarki a kan wannan sakamako da ya nuna ba a dauke da cutar. Haka Allah ya so. Duk wadanda sakamako ya nuna sun kamu, za mu ci gaba da yi masu addu’ar samun lafiya cikin gaggawa daga wannan cuta, ba tare da la’aakari da kasa ba ko kabilanci, matsayi, akidar siyasa ko addini ba.

Sakamakon gwaji ya nuna Ganduje da matarsa basa dauke da cutar Covid-19
Sakamakon gwaji ya nuna Ganduje da matarsa basa dauke da cutar Covid-19
Asali: Facebook

“Muna kuma godiya ga Allah da ya ci gaba da kare jahar, kasa da duniya baki daya daga cutar COVID-19.

“Yayin da muke addu’a ya zama dole mu tabbatar da cewar muna sauraron masana kiwon lafiya a koda yaushe sannan mu yi aiki da shawarwarinsu,” in ji sanarwar.

Ya bukaci jama’a da su lazumci wanke hannayensu a ruwa mai kwaranya da sabulu ko abun kasha kwayoyin cuta, tsaftar muhalli da kuma nisantan taron jama’a.

“Zama a gida shi yafi kyawu. Ina kuma bukatar yan Najeriya da su bi umurnin gwamnatin tarayya sosai wajen takaita yaduwar cutar,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya kuma jadadda jajicewar gwamnati wajen ganin ta dauki matakan kare kai da hada hannu da kungiyoyin da suka kamata da masu ruwa da tsaki domin hana yaduwar cutar COVID-19.

“Hakkinmu ne yaki da COVID-19 ta kowani lungu domin tsiratar da al’umma.

“Mun gode ma Allah da ba a samu bullar cutar ba a Kano har zuwa wannan lokaci. Allah ya kare sauran jihohi a kasar da sauran kasashen duniya da suka kamu,” ya yi addu’a.

Ganduje ya kara da cewar an dauki matakai domin kula da kuma tabbatar ganin an bi dokar rufe iyakokin jahar, inda ya yi gargadin cewa za a hukunta wadanda suka saba.

Gwamnan ya yi godiya ga kwamitin jahar kan COVID-19 da ma’aikatan lafiya a kan jajircewarsu kan yakar coronavirus.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: An jefi jami'an tsaron gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma

A wani labari na daban mun ji cewa wani malamin addinin musulunci a kasar Saudi Arabia ya ce halas mata su kauracewa shimfidar mazajensu wadanda ba su kiyayye ka'idojojin kare kansu daga kamuwa daga muguwar annobar coronavirus kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sheikh Abdulla al-Mutlaq, mamba na kungiyar manyan malaman addinin musulunci a kasar, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambayar da wata ta aiko masa a shirin addinin da ake gudanarwa a talabijin mai suna 'Fatwa' da aka watsa wa a gidan talabijin na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel