Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus

Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus

Wani ma'aikacin jinya a kasar Italiya ya shege budurwarsa likita har sai da ta mutu saboda ita ce sanadin kamuwarsa da cutar coronavirus.

Bayan aikata laifin, Antonio De Pace dan shekara 28 ya kira 'yan sanda inda ya fada musu cewa ya kashe likitar, Lorena Quaranta mai shekaru 27 kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Da 'yan sanda suka isa wurin da abin ya faru, sun tsinci gawar ta a gidansu da ke Italiya yayin da shi kuma De Pace suka gan shi kwance a kasa ya yanka hannunsa amma takwarorinsa sun yi kokarin sun ceto ransa a asibiti.

Masoyan sun kasance suna aiki tare a asibitin Messina a Sicily bayan an bukaci su taimaka sakamakon bullar annobar coronavirus.

Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus
Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Rahotanni sun bayyana cew De Pace ya amsa cewa: "Na kashe ta saboda ta bani coronavirus."

Wata majiya daga 'yan sanda ta ce: "Likita ce matar, kuma tana aiki sosai domin ceto rayuwar mutane. Abin bakin ciki ne."

The sun ta ruwaito cewa an yi wa masoyan biyu gwajin kwayar cutar ta Covid-19 amma sakamakon ya nuna cewa dukkansu biyu ba su dauke da cutar.

Lorena tana daga cikin wadanda suke jajircewa wurin wayar da kan al'umma game da coronavirus a dandalin sada zumunta tun bayan bullar annobar.

Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus
Ma'aikacin jinya ya kashe budurwarsa likita saboda ta harbe shi da coronavirus
Asali: Twitter

A shafinta na Facebook, ta shawarci al'umma su rika nuna wa juna soyayya da kauna kana su rika girmama kansu kana su rika kiyaye dokokin da sai sa kaucew kamuwa da muguwar kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164