Gwamnoni 3 sun kamu da cutar COVID-19, da-dama sun yi gum
Yayin da ake fama da cutar Coronavirus, wani rahoto da Daily Trust ta fitar ya nuna cewa har yanzu babu wanda ya san halin da Gwamnonin jihohi 20 su ke ciki a Najeriya.
Daga cikin Gwamnoni 36 da ake da su, 20 ba su fadawa Duniya sakamakon gwajin COVID-19 da su ka yi ba. Jaridar ta fitar da rahoton binciken ne a Ranar 2 ga Watan Afrilu, 2020.
Gwamnonin jihohin da ba su fadi halin da su ke ciki ba su ne na: Akwa Ibom, Ribas, Delta, Enugu, Zamfara, Kano, Jigawa, Adamawa, Taraba, Gombe da kuma Gwamnan jihar Legas.
Ragowar wadannan gwamnoni sun hada da Sokoto, Yobe, Kwara, Benuwai, Ebonyi, Kogi, Imo da Abia. Ku na sane cewa ta tabbata gwamnoni uku sun kamu da cutar Coronavirus.
Bayan an yi gwaji, Gwamnonin da su ke dauke da wannan cuta su ne: Bala Abdulkadir Mohammed na Bauchi; Nasir El-Rufai na Kaduna; da gwamna Seyi Makinde na Oyo.
KU KARANTA: COVID-19: Sarkin Kano ya yi kira ga Jama'a su zauna cikin tsabta
Akwai gwamnoni 13 da aka tabbatar cewa ba su dauke da wannan cuta. Wadannan gwamnoni su ne na Kebbi, Katsina, Osun, Ekiti, Edo, Bayelsa, Ogun, Ondo, Nasarawa, da jihar Neja.
Amma irinsu gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ba su shaidawa jama’a ko su na dauke da COVID-19. Shi ma gwamnan jihar Imo watau Hope Uzodinma, ya yi gum da lamarin.
Haka zalika Babajide Sanwo – Olu bai bayyana sakamakon gwajinsa ba idan har yayi. A Filato da Yobe, jama’a ba su da labarin ko Simon Lalong da Mala Buni sun yi gwajin wannan cuta.
Gwamnonin Adamawa da Benuwai ba su yi wanna gwaji ba tukuna. Babu tabbacin ko an yi wa gwamnonin Jigawa, Taraba da kuma Zamfara gwajin cutar COVID-19 a halin yanzu.
Gwamnonin jihohin Kuros Riba, Anambra da Borno su na cikin wadanda ba su kamu da wannan cuta ba. Gwamnan jihar Kano ya yi gwajin, amma dai sakamakonsa bai fito ba tukuna.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng