Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19

Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19

- Dakta Shifa M. Mohammed, matashiyar likita 'yar asalin kasar Indiya, ta dakatar da aurenta don ta cigaba da bawa marasa lafiya kulawa

- Matashiyar likitar, mai shekaru 23, na kula da masu dauke da kwayar cutar covid-19 da aka killace a wata cibiya, amma ta zabi kasancewa da su a kan ta tafi sha'anin aurenta

- A cewar Dakta Shifa, aure zai iya jira zuwa wani lokaci na gaba, amma marasa lafiyar da take kula da su, ba zasu iya jira ba

Wata matashiyar likita mai shekaru 23 a duniya da aka bayyana sunanta da Shifa M. Mohammed, ta daga ranar daurin aurenta domin ta samu natsuwa tare da tattara hankalinta a kan masu dauke da kwayar da cutar covid-19 da take kula da su.

Dakta Shifa, kwararriya a bangaren tiyata, ta zabi kasancewa a wurin aikinta na kula na masu cutar coronavirus a ranar daurin aurenta, ranar 29 ga watan Maris.

Matashiyar likitar, mai shekaru 23, ta na kula da masu dauke da kwayar da cutar da aka killace ne a asibitin da take aiki; asibitin kwalejin likitanci na Pariyaram da ke garin Kannur, kamar yadda jaridar kasar Indiya, 'Hindustan Times', ta rawaito.

Matashiyar likita ta dakatar da aurenta don cigaba ta ceton rayuwar masu cutar covid-19

Dakta Shifa
Source: UGC

Rahoton jaridar ya bayyana cewa Dakta Shifa ta bayyana cewa aure zai iya jira, a saboda haka ta zabi bayar da lokacinta domin ceton rayuwar mutanen da cutar covid-19 ta kwantar.

DUBA WANNAN: Ramuwar gayya: Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

Ita da kanta matashiyar likitar, ta bayyanawa manema labarai cewa, "tabbas da gaske ne, na zabi zama a wurin aikina tare da marasa lafiya da aka killace a ranar da ya kamata ta kasance ranar aurena, lamarin da yasa har wasu abokan aikina ke tsokana ta. Na fi jin dadin ceton rayuwar marasa lafiya fiye da komai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel