Yanzu Yanzu: An sake samun sabbin mutane 23 da suka kamu da coronavirus a Najeriya

Yanzu Yanzu: An sake samun sabbin mutane 23 da suka kamu da coronavirus a Najeriya

- Hukumar da ke kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta sanar da cewa an sake samun karin sabbin mutane 23 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar

- Hukumar ta ce tara daga cikin mutanen sun kasance a jahar Lagas ne, bakwai daga Abuja inda biyar suka fito daga jihar Akwa Ibom sai kuma mutum daya daga jahar Bauchi

- Zuwa yanzu jimlar mutane 174 ne suka kamu da cutar a kasar

Rahoto da muka samu daga hukumar da ke kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ya nuna cewa an sake samun karin sabbin mutane 23 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce tara daga cikin mutanen sun kasance a jahar Lagas ne, bakwai daga Abuja inda biyar suka fito daga jihar Akwa Ibom sai kuma mutum daya daga jahar Bauchi.

Yanzu haka jumullar mutane da ke dauke da cutar a kasar sun zama 174, an salami mutane tara yayinda biyu suka mutu.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Gwamnatin Taraba ta yi umurnin rufe kasuwanni da hana sallar Juma’a da zuwa coci

A gefe daya mun ji cewa wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

"Mun samu labarin cewa ya gudu cikin Bida, kuma muna biye da shi yanzu. Mambobin hukumar yaki da COVID-19 da jami'an ma'aikatar lafiya na Bida yanzu domin nemansa da kuma tabbatar da cewa ya yi abinda cibiyar NCDC ta umurcesa."

Kwamishanan ya kara da cewa an killace wasu mutane biyu da suka dawo daga kasar Birtaniya da Canada a garin Kontagora kuma ana gwada su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel