Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

Bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa dakarun sojin kasar Chad harin kwanton bauna a cikin makon da ya gabata, dakarun sojojin kasar ta Chadi sun kai wa mayakan kungiyar harin ramuwar gayya a cikin satin da muke ciki.

A yayin da yake ganawa da kwamandojin rundunar sojojin hadin gwuiwa (MNJTF) a Baga ta jihar Borno bayan harin daka kai wa sojojin kasarsa, shugaban kasar Chadi, Idriss Derby, ya bawa sojojin umarnin su fara wani atisaye, ba tare da nuna tausayi ba, a yankin tafkin tekun Chadi.

A wani faifan bidiyo da PRNigeria ta samu, an ga sojojin kasar Chadi suna wakokin karawa junansu karfin gwuiwa yayin da suke harbawa mayakan kungiyar Boko Haram makami mai nisan zango (RPG) a lokacin da suke kazamar musayar wuta.

DUBA WANNAN: Sakon faifan bidiyo zuwa ga Buhari: Janar a rundunar ya fadi gaskiyar halin da suke ciki a Borno

A wani faifan bidiyon na daban, an ga dakarun sojojin na kasar Chadi suna tattaka mayakan kungiyar Boko Haram da suka zube a kasa jina-jina da kuma wadanda suka mutu bayan an fafata musayar wuta a tsakani.

Kalli faifan bidiyon a kasa:

Dangane da hakan ne, shugaban tsohuwar kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon sakon sautin murya domin karawa mayakansa karfin gwuiwa tare da yi wa shugaban kasar Chadi barazana.

A cikin faifan sautin muryar da Shekau ya yi musamman saboda shugaba Deby, Shekau ya gargade shi cikin harshen Hausa a kan cewa, "kar ka yi tunanin cewa ka yi yake-yake a baya ka samu nasara, ba zaka samu galaba a kanmu ba saboda mu Jihadi muke yi".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel