Covid-19: Gwamnatin Taraba ta yi umurnin rufe kasuwanni da hana sallar Juma’a da zuwa coci

Covid-19: Gwamnatin Taraba ta yi umurnin rufe kasuwanni da hana sallar Juma’a da zuwa coci

Gwamna Darius Ishaku na jahar Taraba ya yi umurnin rufe dukkanin kasuwannin jahar ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma yi umurnin hana sallar Juma’a da zuwa coci a ranar Lahadi.

Gwamnan ya bayar da umurnin ne a cikin wani jawabi daga mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu a ranar Laraba, 1 ya watan Afrilu.

Darius ya bayyana cewa an yi sanarwar ne domin yiwa mutanen jahar karin bayani kan lamarin Coronavirus a jahar.

Covid-19: Gwamnatin Taraba ta yi umurnin rufe kasuwanni da hana sallar Juma’a da zuwa coci
Covid-19: Gwamnatin Taraba ta yi umurnin rufe kasuwanni da hana sallar Juma’a da zuwa coci
Asali: Twitter

Ya ce an sanar da yan kasuwa kafin gwamnati ta yanke hukuncin rufe kasuwanni da shaguna a jahar daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2020.

Ishaku ya ce zuwa yanzu ba a samu bullar COVID-19 a jahar ba.

Ya ce shagunan da ke siyar da muhimman abubuwan bukata kamar shagunan abinci, na magunguna da gidajen mai me kawai za a bari su yi aiki.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jama'a amfani da takunkumin rufe fuska saboda covid-19

Ya kuma bayyana cewar an mayar da cibiyar lafiya ta tarayya da ke Jalingo da asibitin kwararru na Jalingo a matsayin wajen killace mutane, inda ya kara da cewar an tura kudade domin zuba kayayyakin aiki a cibiyoyin guda biyu.

Gwamnan ya kuma yi gargadi a kan boye kayan abinci da tsadar kayayyakin.

A gefe guda mun ji cewa Kamfanonin samar da wutan lantarkin Najeriya GenCos, sun yi alkawarin tabbatar da cewa ana cigaba da samun isasshen wuta a kasar wannan lokacin na zama a gida.

Sakatariyar kungiyar kamfanonin, Joy Ogaji, ta bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Gaji ta ce GenCos na hada kai da juna wajen tabbatar da cewa yan Najeriya sun samu isasshen wutan lantarki yayin annobar Coronavirus.

Tace"Mun kara yawan wutan da muke samarwa zuwa Migawat 4,024 tun lokacin da aka samu bullar cutar ranar 27 ga Febrairu."

"Yayinda muke cigaba da ganin ana cigaba da aiki, GenCos na iyakan kokarin tabbatar da cewa aiki na tafiya saboda kada hakan ya shafi tattalin arziki."

Hukumar daidaita farashin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce ta dakatar da karin kudin wutar lantarki wanda ta tsara zai fara aiki a ranar 1 ga watan Afirilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel