Abin da ya sa Gwamna Ben Ayade ya ki barin ‘Yan Amurka shiga jihar Kuros-Riba

Abin da ya sa Gwamna Ben Ayade ya ki barin ‘Yan Amurka shiga jihar Kuros-Riba

Mai magana da yawun bakin gwamnan Kuros Riba, Christian Ita, ya bayyana cewa gwamnati ta hana wasu mutanen kasar Amurka shigowa jihar a farkon makon nan.

Gwamnatin Farfesa Ben Ayade ta haramtawa wadannan Amurkawa da ke aiki a kamfanonin mai shiga babban birnin Kalaba ne a Ranar Litinin, 30 ga Watan Maris, 2020.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoton jawabin da Christian Ita ya yi a Ranar Talata. Ita ya bayyana cewa dalilin da ya sa Mai gidansa, Ben Ayade, ya dauki wannan mataki.

A cewar Hadimin gwamnan, rufe iyakokin shigowa jihar Kuros Riba da aka yi ne ya sa ba a kyale wadannan baki sun shigo jihar kai tsaye ba, yayin da ake fama da annoba.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan ya na cikin matakan da ya dauka na garkame duk wata kafar shigowa jihar Kuros Riba ta hanyoyin ruwa, da kasa da ma ta samaniya.

KU KARANTA: NCDC ta na laluben mutum 5000 da su ka yi hulda da masu Coronavirus

Abin da ya sa Gwamna Ben Ayade ya ki barin ‘Yan Amurka shiga jihar Kuros-Riba
Gwamna Ayade ya ce babu wanda zai shigo jiharsa sai ya yi gwaji
Asali: Twitter

Mai magana a madadin Mai girma gwamna Ayade ya ce an bukaci wadannan Bayin Allah su fara zuwa Garin Abuja ko kuma Legas domin a yi masu gwajin kwayar cutar COVID-19.

Gwamnan ya bayyana cewa dole sai an yi wa Amurkawan gwaji domin tabbatar da ko su na dauke da kwayar COVID-19 kafin a ba su damar shigowa jihar a wannan marra.

A makon nan ne mu ka ji labarin cewa ofishin Jakadancin kasar Amurka ta fara dauke mutanen ta da ke cikin Najeriya. An dauki wannan mataki ne bayan barkewar Coronavirus.

A halin yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta dauko mutanenta da ke kasashen ketare ba. Kawo yanzu cutar COVID-19 ta kashe mutane fiye da 30, 000 a cikin kasashen Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng