Gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jama'a amfani da takunkumin rufe fuska saboda covid-19

Gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jama'a amfani da takunkumin rufe fuska saboda covid-19

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar tilasta wa dukkanin yan Najeriya amfani da takunkumin rufe fuska domin hana yaduwar cutar COVID-19, wanda ke ci gaba da hauhawa.

Har ila yau tana sake duba yarjejeniyar rufe jigohin Lagas da Ogun da kuma birnin tarayya na kwanaki 14, jaridar Thisday ta ruwaito.

Domin kara kaimi wajen warkar da wadanda suka harbu da cutar, gwamnati ta dawo da ma’aikatan lafiya da suka yi ritaya inda a yanzu ake horar dasu domin su taimaka wajen kula da warkar da wadanda suka kamu.

Sauran matakan yakar annobar sun hada da bude karin cibiyoyin gwaji domin Najeriya ta samu damar yiwa mutane 1,500 gwaji a kullun a kokarinta na gaggawan gano wadanda suka kamu.

Gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jama'a amfani da takunkumin rufe fuska saboda covid-19

Gwamnatin tarayya za ta tilasta wa jama'a amfani da takunkumin rufe fuska saboda covid-19
Source: UGC

Alkalma daga cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka na Najeriya ya nuna ceewa zuwa yanzu kasar ta yiwa zama da mutane 2,000 gwaji tun bayan barkewar annobar a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Gwamnatin tarayyar na kuma duba yiwuwar bayar da tallafi ga mutane miliyan 11 sakamakon wahalhalun da COVID-19 ya jefa mutane ciki.

Da yake magana a jiya Talata a Abuja a wani taron manema labarai na kwamitin Shugaban kasa kan coronavirus, Darakta Janar na NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu, ya ce hukumar na duba yiwuwar tursasa amfani da takunkumin fuska domin yaki da hana yaduwar cutar.

Ihekweazu ya bayyana cewa koda dai cibiyar lafiya ta duniya ta bayar da shawarar cewa ma’aikatan lafiya ne kadai ya kamata su yi amfani da takunkumin fuskar, NCDC na iya ba da shawarar a fara amfani dashi a kasa baki daya domin kare kai daga kwasar cutar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Saudiyya ta umarci kasashe su dakatar da karbar kudin aikin Hajjin bana

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kamfanonin samar da wutan lantarkin Najeriya GenCos, sun yi alkawarin tabbatar da cewa ana cigaba da samun isasshen wuta a kasar wannan lokacin na zama a gida.

Sakatariyar kungiyar kamfanonin, Joy Ogaji, ta bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel