Wasa na ke yi, na san COVID-19 ba karya ba ce - Gwamna Makinde

Wasa na ke yi, na san COVID-19 ba karya ba ce - Gwamna Makinde

- Gwamna Seyi Makinde ya ce yan adawa ne suka yiwa ba’a da ya yi game da bullar coronavirus wata fassara na daban

- Kafin a gwada shi, Makinde, yayinda ya ke jawabi a wani gangamin PDP Ibadan, ya ce babu coronavirus a jam’iyyarsa

- Da ya ke kare furucinsa, gwamnan ya ce COVID-19 gaskiya ce, kuma ya zama dole mutane su bi matakan kare kai

Seyi Makinde, gwamnan jahar Oyo, ya yi karin haske game da lamarin da ya alakanta shi da inda yake faadin cewa yana kokwanto a kan ko da gaske akwai coronavirus.

Da yake magana a wayar tarho da Fresh FM a ranar Talata, 31 ga watan Maris, Makinde ya ce an yiwa ba’a da ya yi kan cewa babu coronavirus a jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP), mummunan fahimta.

Coronavirus: Ba’a kawai nayi a kan da Covid-19 amma cutar gaskiya ce - Makinde
Coronavirus: Ba’a kawai nayi a kan da Covid-19 amma cutar gaskiya ce - Makinde
Asali: UGC

Legit.ng ta tuna cewa gwamnan Oyo, yayinda ya ke magana a wani gangamin PDP a ranar Laraba, 18 ga watan Maris, a Ibadan, babbar birnin jahar Oyo a dakin taro na Mapo domin tarban wadanda suka sauya sheka, ya yi ba’a game da gaskiyan COVID-19.

Gwamnan ya ce: “Sun ce kada mu yi gangami saboda coronavirus. Shugabansu ne y ace akwai coronavirus a jam’iyyarsu, eh ko aá? Shin kun yi amfani da abun kashe kwayoyin cutarku? Babu coronavirus a namu jam’iyyar.”

Yan kwanaki bayan Makinde ya bayar da hakuri kan gudanar da gangamin na PDP biyo bayan samun karin wadanda suka kamu da cutar a kasa, shima sai gashi ya kamu da cutar.

A yanzu gwamnan ya kare kansa biyo bayan cacakar da ya sha bayan an sanar da cewar ya kamu.

Makinde ya ce yan adawa ne suka yiwa ba’a da ya yi game da bullar coronavirus wata fassara na daban.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Gwamnan ya jadadda cewar COVID-19 gaskiya ce, kuma ya zama dole mutane su bi matakan kare kai.

Ya kuma bayyana cewa jahar Oyo bata rufe harkokinta baki daya ba amma gwamnati za ta ci gaba da kula da lamarin a jahar.

A wani labarin kuma mun ji cewa n gano cewa wata marar lafiya mai dauke da cutar covid-19 ta tsere daga inda aka killace ta a kasar Ghana.

Kamar yadda jaridar Ghana City News ta bayyana, mara lafiyan na daya daga cikin mutane takwas 'yan asalin kasar da kwanan nan aka gano suna dauke da muguwar cutar a Ghana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng