Wata sabuwa: Mai dauke da cutar Coronavirus a Bauchi ya ki zaman Asibiti, ya koma gida

Wata sabuwa: Mai dauke da cutar Coronavirus a Bauchi ya ki zaman Asibiti, ya koma gida

Wani babban mutumi da aka tabbatar yana dauke da annobar cutar Coronavirus a jahar Bauchi ya yi tsallen badake inda ya tsaya kai da fata lallai ba zai cigaba da zama a wajen da ake killace masu dauke da cutar ba.

Daily Trust ta ruwaito wannan mutumi wanda majiyoyi suka tabbatar abokin gwamnan jahar Bauchi ne, watau Sanata Bala Muhammad wanda shi kansa a yanzu haka yana can a killace sakamakon kamuwa da cutar, ya tsere da asibitin, ya kuma koma gida wajen iyalansa.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnati za ta yi ma yan Najeriya 1,500 gwaji a duk rana

Sai dai majiyar ta ruwaito dalilin da wannan mutumi na arcewa daga wajen killacewar shi ne saboda kazantar dake wurin, domin kuwa an jiyo shi yana cewa: “Wannan wurin ya yi kazanta da yawa, ba zan iya zama a nan ba.”

Wata majiya daga ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sakamakon wannan bore da mutumin yayi, kwamitin ko-ta-kwana mai kula da Coronavirus a jahar ta gudanar da wani taron gaggawa.

Daga karshen taron, kwamitin ta yanke shawarar sauya wurin killace masu dauke da cutar zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa wanda ya fi kyau sama da tsohon wurin.

“A yanzu dai ya amince zai koma sabon wurin killace masu dauke da cutar dake asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, kuma tuni an aika da motar daukan marasa lafiya zuwa gidansa dake GRA domin dauko shi.” Inji majiyar.

Koda a ka tuntubi kwamishinan kiwon lafiya na jahar Bauchi, Dakta Aliyu Muhammed Toro game da lamarin, bai musanta ba, amma yace a yanzu haka mutumin yana zaune a asibitin.

A wani labari kuma, karamin ministan kiwon lafiya, Dakta Olurunnimbe Mamore ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kashe kimanin naira dubu 10 wajen gudanar da gwajin Coronavirus ta hanyar amfani da tsarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, dake bayar da gamsashshen sakamako.

Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace amma gwamnati ba wai ta damu da kashe kudin bane, tunda dai ana samun sahihin sakamako.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel