Coronavirus: Najeriya ta rasa wani babban likitanta da ke kula da marasa lafiya a Ingila

Coronavirus: Najeriya ta rasa wani babban likitanta da ke kula da marasa lafiya a Ingila

Najeriya ta rasa wani babban likitanta a kasar waje, Alfa Saadu, wanda ya kasance a Ingila yana kula da mutanen da suka kamu da cutar COCID-19 wanda aka fi sani da coronavirus.

Wasu da suka san liitan na nan suna jimamin mutuwarsa a soshiyal midiya.

Legit.ng ta fahimci cewa ya shiga sahun likitocin Ingila a matsayin likitan sa kai lokacin da annobar ta balle a kasar. Shima ya kamu a cutar daga baya.

Daya daga cikin masu alhinin mutuwar nasa ya kira shi a matsayin salihin mutum mai tarin hikima. “A kullun kana jaircewa kan aiki da kuma taimako kai da fata.”

Coronavirus: Najeriya ta rasa wani babban likitanta da ke kula da marasa lafiya a Ingila
Coronavirus: Najeriya ta rasa wani babban likitanta da ke kula da marasa lafiya a Ingila
Asali: UGC

A nashi bangaren, Bukola Saraki, tsohon Shugaban majalisar dattawa ya ce: “Ina mika ta’aziyyata ga iyalan marigayi Dr. Alfa Sa’adu, mutanen Pategi da jahar Kwara na alhinin mutuwar babban likita wanda ya mutu a birnin Landan a safiyar yau.

“Marigayi Dr Sa’adu ya sama wa mutanenmu girma na shugabanci a kasar waje yayin da ya yi aiki tsawon shekaru da dama a matsayin Shugaban kungiyar jahar Kwara a Najeriya (Kwasang UK).

“A gida, ya kasance Shugaba kuma wanda ke rike da sarauta a matsayin Galadiman Pategi. Shakka babu za a yi kewarsa.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi

Idan za ku tuna a baya mun kawo maku cewa Karamin ministan harkokin kiwon lafiya, Adeleke Mamora ya bayyana cewa an samu wani likita dan Najeriya da ya rasa ransa a sakamakon annobar cutar Coronavirus a kasar Canada.

Daily Nigerian ta ruwaito Minista Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake bayar da jawabi a kan cutar Coronavirus ga manema labaru inda yace sunan wannan likita dan Najeriya Olumide Okunuga.

“Ya kamata kowa ya zama mai lura da ankara, na ji jama’a na cewa wai bakar fata na da kariya daga cutar Coronavirus, wai ba za ta iya cutar damu ba, don haka nake shaida mana cewa bakar fata kuma dan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar.

“Mun samu labarin wani likita dan Najeriya dake zama a kasar Italiya wanda ya mutu a sakamakon cutar, don haka akwai bukatar mu yi taka tsantsan game da sauraron batutuwan da basu tabbata ba.” Inji shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel