An sauya manyan kwamandojin soji da ke jagorantar yaki da 'yan Boko Haram

An sauya manyan kwamandojin soji da ke jagorantar yaki da 'yan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya ta sauya manyan kwamandojinta da ke jagorantar yaki da yan ta’addan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Hukumar sojin ta nada Faruk Yahaya a matsayin sabon kwamandan Operation Lafiya Dole, da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas.

Yahaya wanda ya kasance Manjo Janar, wanda kafin nadin nasa ya kasance kwamandan sojojin sashi na 1 a Kaduna, zai maye gurbin Olusegun Adeniyi wanda ke rike da ragamar tun watan Agusta.

A gagarumin sauyin janarori da sauran manyan jami’ai da aka yi, Adeniyi zai koma aiki a cibiyar albarkatu na rundunar sojin Najeriya Abuja a matsayin babban mai bincike.

An sauya manyan kwamandojin soji da ke jagorantar yaki da 'yan Boko Haram

An sauya manyan kwamandojin soji da ke jagorantar yaki da 'yan Boko Haram
Source: UGC

A wani jawabi da ya saki a ranar Talata, 31 ga watan Maris, kakakin rundunar sojin, Sagir Musa ya ce sauye-sauyen wanda Tukur Buratai, Shugaban hafsan soji ya aminta dashi, ya ce an yi shirin ne domin kaw sauyi a tsarin don ci gaban rundunar.

“Gagarumin sauyin sun hada da: nadin Manjo Janar ACC Agundu daga runduna na musamman na Operation SAFE HAVEN Jos zuwa cibiyar albarkatun rundunar sojin Najeriya (NARC) Abuja a matsayin babban mai bincike, Manjo Janar HI Bature daga hedkwatar tsaro ofishin majalisar dokokin tarayya zuwa hedkwatar rundunar soji sashin harkokin soji sannan aka nada Shugaban harkokin soji Manjo Janar UM Mohammed daga sashin NAPL zuwa ofishin Shugaban rundunar soji sannan aka nada mai ba da shawara na musamman kan jami’ar sojin Najeriya Biu zuwa mataimakin Shugaban kwamitin amintattu na NAPL, yayinda tsohon mai ba da shawara na musamman kan jami’ar sojin Najeriya Biu, Manjo Janar CC Okonkwo ya koma sashin STF Operation SAFE HAVEN Jos a matsayin kwamanda.

“Manjo Janar F Yahaya daga hedkwatar 1 Division Kaduna zuwa hedkwatar Operation LAFIYA DOLE (OPLD) Maiduguri sannan aka nada shi a matsayin kwamanda, yayinda aka dauke da Manjo Janar OG Adeniyi daga Theatre Command OPLD Maiduguri zuwa sashin NARC a matsayin babban mai bincike, manjo Janar S Idris daga sashi 2 OPLD Damaturu- jahar Yobe zuwa Hedkwatar rundunar soji a Abuja sannan aka nada shi a matsayin Darakta,” in ji sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi

Sauran da lamarin ya shafa sune: Manjo Janar AA Adesope daga ofishin Shugaban hafsan sojin Najeriya zuwa NAPL sannan aka nada shi a matsayin Manajan Darakta na reshen, Manjo Janar MG Ali daga hedkwatar rundunar OPLD Maiduguri zuwa hedkwatar runduna na musamman Doma, jahar Nasarawa a matsayin kwamanda yayinda tsohon Shugaban harkokin ADQ Abuja Manjo Janar US Mohammed ya koma sashin 1 Division Kaduna a matsayin kwamanda.

Rundunar ta ce dukkanin nade-naden zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilu 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel