Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi

Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi

- An sake samun wani dake dauke da cutar Coronavirus a jahar Bauchi

- Mataimakin gwamnan jahar, Sanata Baba Tela ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 31 ga watan Maris

- Mutumin mai shekara 55 a duniya ya zama mutum na uku da aka samu da cutar a jahar

Rahotanni sun kawo cewa an sake samun wani dake dauke da cutar Coronavirus a jahar Bauchi.

Mataimakin gwamnan jahar, Sanata Baba Tela ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 31 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi
Yanzu Yanzu: An sake samun mutum na uku da ke dauke da coronavirus a Bauchi
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai a kan lamarin a jahar, Tela, wanda ya kuma kasance Shugaban kwamitin Covid-19, ya ce mutumin da aka samu da cutar ya kasance dan shekara 55.

A yanzu mutane uku kenan aka tabbatar da suna dauke da cutar a jahar zuwa yanzu.

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Ekiti ta sanar da cewa an sallami mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus da mai kula da shi daga cibiyar killace masu cutar a jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita ranar Talata inda tace mutumin ya tafi gida bayan kwashe kwanaki 12 a killace.

Kwamishanar kiwon lafiyan jihar, Dakta Mojisola Yaya-Kolade, da wata jami'ar UNICEF suka rakasu bayan an sallamesu.

KU KARANTA KUMA: Abun da ya kamata ku sani game da kasashen Afrika 6 da ba a samu bullar coronavirus ba

Har ila yau mun samu labari cewa Sakamakon gwajin kwayar cutar Covid-19 da aka yi wa Sufeta Janar (IGP) na Rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar.

IGP din ya samu sakamakon gwajinsa da safiyar yau 31 ga watan Maris bayan an dauki jininsa domin gwajin a ranar Juma'a 27 ga watan Maris na 2020 kamar yadda Kakakin rundunar, Frank Mba ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.

Mba shima ya bayyana cewa ya yi gwajin kuma sakamakon ya nuna baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel