Duniya ta yi dadi: Kansila ya aure mata 2 a rana daya a jahar Nassarawa
Yayin da ake ta kokarin dabbaka dokar tsayuwa nesa nesa da juna a Najeriya gaba daya sakamakon bullar annobar nan mai toshe numfashin dan Adam watau Coronavirus, shi kuwa wani kansila rabashewarsa ya yi ta hanyar auren mata 2 a rana 1.
Daily Trust ta ruwaito wannan kansila mai suna Ibrahim Oboshi yana wakiltar mazabar Iwogu ne a majalisar karamar hukumar Keana ta jahar Nassarawa, kuma ya auri masoyansa biyu Nazira Ozegya da Rabi Akosi a rana daya.
KU KARANTA: Gwamna Zulum ya garkame Borno, yace Coronavirus ta fi karfin Boko Haram
Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito alamu sun nuna duka yan matan biyu tare da mijinsu ne suka tsara auren a haka, saboda hatta a jikin katin gayyatar daurin auren sunayensu ne a rubuce duka.
Kansila Ibrahim Oboshi ya auri Nazira Ozegya ne da misalin karfe 10 na safiyar Asabar 28 ga watan Maris, yayin da ya auri Rabi Akoshi da misalin karfe 12 na ranar Asabar, 28 ga watan Maris.
Haka kuma dukkaninsu suka taru suka dauki hotunan aure tare, kuma aka kai su gidan aurensu daya a rana daya, a yanzu haka dai sabbin amaren sun shiga gidan mijinsu Ibrahim, wanda koda yake kansila ne, amma yace shi manomi ne.
A wani labarin kuma, a kokarinta na rangwanta ma al’ummar Najeriya bisa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon barkewar annaobar Coronavirus, gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanonin sadarwa su sassauta ma yan Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isah Ali Pantami, wanda ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a daren Talata, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng