Abun da ya kamata ku sani game da kasashen Afrika 6 da ba a samu bullar coronavirus ba

Abun da ya kamata ku sani game da kasashen Afrika 6 da ba a samu bullar coronavirus ba

Kasashen Afrika shida na cikin wasu yan tsirarun kasashen duniya da basu samu bullar cutar Coronavirus ba.

Kusan kowace kasa ta samu bullar annobar wacce ta game duniya.

A nahiyar Afrika mahukunta sun yi ikirarin cewa Ubangiji ya tsiratar dasu yayinda wasu ke cewa rashin zarya a kasashensu daga ketare ya tsiratar dasu, sai dai kuma a wasu ana tsoron cewa rashin gwaji ne ke boye gaskiyar lamarin.

Abun da ya kamata ku sani game da kasashen Afrika 6 da ba a samu bullar coronavirus ba
Abun da ya kamata ku sani game da kasashen Afrika 6 da ba a samu bullar coronavirus ba
Asali: UGC

1. Sudan ta kudu

Kasar wacce ke a Afrika ta gabas na farfadowa daga yakin basasa na shekara shida da matsanacin yunwa, rashin lafiya da karancin kayayyakin more rayuwa, masu lura na tsoron annobar na iya kawo tarin halaka.

Docta Angok Gordon Kuol, daya daga cikin wadanda ke jagorantar yaki da cutar, ya ce kasar ta gudanar da gwaje-gwaje 12 inda ba a samu ko mutum guda da ke da cutar ba.

Ya ce dalilin da yasa cutar bai isa kudancin Sudan ba har yanzu shine sanadiyar rashin yawan shiga kasar.

“Yan tsirarun jiragen kasa ke shigowa kudancin Sudan kuma mafi akasarin kasashen da suka kamu a yau ya kasance ta dalilin masu zuwa daga kadashen Turai.”

Ya ce babban abun damuwa sune yan kasashen waje da ke aiki da manyan kungiyoyi masu zaman kansu da na agaji ko mutanen da ke tsallake iyakoki daga kasashen waje.

Sudan ta Kudu ta rufe makarantu, ta haramta taron aure, jana’iza da wasanni sannan ta hana jiragen sama daga kasashen da ke fama da cutar shiga cikinta. An rufe kasuwanci da masu muhimmanci bane sannan ta takaita zirga-zirga.

A yanzu haka kasar na iya yiwa mutane 500 gwaji sannan tana da cibiyar killace mutane guda daya da gadaje guda 24.

2. Burundi

A Burundi, wacce ke tunkarar zaben kasa baki daya a watan Mayu, hukumomi sun yi godiya ga matakin gaggawa a matsayin abunda ya hana samun wanda ya kamu da cutar.

“Gwamnatin ta yi godiya ga Allah mai iko da ya kare Burundi,” kakakin gwamnati Prosper Ntahorwamiye ya bayyana a talbijin din kasa a makon da ya gabata.

Hakazalika ya soki wadanda ke yada jita-jitan cewa Burundi bata da karfin yin gwajin cutar, ko kuma rade-radin cewa cutar na yaduwa ba tare da an sani ba.

An dauki wasu matakai kamar su dakatar da jiragen waje da sanya tashoshin wanke hannu a mashigin bankuna da gidajen cin abinci a Bujumbura.

Sai dai likitoci da dama sun nuna damuwa.

“Babu rahoton wanda ya kamu a Burundi saboda ba a gwada kowa ba,” inji wani likitan Burundi da ya nemi a sakaya sunansa.

3. Sao Tome and Principe

São Tomé and Principe ta kasance wata yar karamar kasa da ke lullube da jeji. Ba a samu lamarin Coronavirus ba saboda ba ta yi gwaji ba, a cewar wakiliyar hukumar lafiya ta duniya Anne Ancia.

Sai dai “Muna ci gaba da shirye-shirye,” da kimanin mutane 100 a killace bayan sun dawo daga kasashen da suka kamu, sannan hukumar WHO na zuba idanu kan masu ciwon pneumonia.

Kasar na kokarin ganin ta hana cutar shiga cikinta domin tana da gadajenmarasa lafiya na ICU guda hudu ne yayinda ya ke da mutanen kusan 200,000 a cikinta, sannan tuni ta riga ta rufe iyakokinta duk da muhimmancin yawon bude ido ga tattalin arzikin kasar.

4. Malawi

Kakakin ma’aikatar lafiya na Malawi, Joshua Malango ya yi jifa da tsoron cewa ko Malawi bata samu bullar cutar bane saboda rashin kayan gwaji: “Muna da kayan gwaji a Malawi kuma muna yin gwajin”.

Dr Bridget Malewezi daga majalisar likitoci ta bayyana wa AFP cewa yayinda “bamu shirya wa cutar ba 100 bisa 100”, gwamnati na shirin ko ta kwana a kan cutar.

Ya bayyana cewa kila zuwa dan lokaci kafin cutar ya shiga Malawi.

Malawi ta bukaci mutanen da suka fito daga kasashen da lamarin ya faru da su killace kansu domin hana yaduwar cutar a kasar.

KU KAANTA KUMA: Covid-19: Gwamna Umahi ya bayar da umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin tserewa daga asibiti

5. Lesotho

Lesotho wacce ta kasance wata alkarya kusa da Afrika ta Kudu da mutane miliyan biyu kacal, ta rufe kasarta a ranar Litinin duk da cewar ba a samu bullar cutar ba.

Kasar ba ta da kayan gwaji sai a makon da ya gabata sannan ta samu bayan ta damu tallafi daga mai kudin kasar China, Jack Ma.

Hukumomi sun tattaro cewa an samu wasu lamura takwas da ake zargin cutar ce wanda ba a yiwa gwaji ba sannan cewa ana sa ran samun sakamakon farko nan ba da jimawa ba.

6. Comoros

Kasar Comoros da ke a tsakanin Madagascar da Mozambique na ba a samu bullar cutar ba, a cewar ma’aikatar lafiya.

Wani likita a babbar birnin kasar Moroni, Dr Abdou Ada, ya yi mamakin ko yawan amfani da maganin zazzabin cizon sauro ne ya haifar da hakan.Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel