Yussuf Buba: mamba a majalisar wakilai ya sadaukar da albashinsa ga jama'arsa har zuwa karshen annobar covid-19

Yussuf Buba: mamba a majalisar wakilai ya sadaukar da albashinsa ga jama'arsa har zuwa karshen annobar covid-19

Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan harkokin kasashen ketare, Yussuf Buba, dan jam'iyyar APC, ya kafa wata gidauniya tare da sadaukar da dukkan albashinsa na kowanne wata ga jama'arsa domin rage musu radadin matsin da annobar cutar covid-19 ta haifar.

A wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja, Buba ya bayyana cewa gidauniyarsa, wacce ya sakawa suna 'Yusuf Captain Buba coronavirus Trust Fund', za ta samar da kayan kare kai daga kamuwa da kwayar cutar coronavirus ga jama'ar mazabarsa da ke jihar Adamawa.

Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Gombi da Honng, ya ce akwai bukatar kyakyawan shiri tare da samar da sahihan bayanai ga jama'a domin yakar kwayar cutar.

"Nasara tana bukatar shiri, a saboda haka dole mu yi damarar yaki da wannan sabuwar cuta.

Yussuf Buba: mamba a majalisar wakilai ya sadaukar da albashinsa ga jama'arsa har zuwa karshen annobar covid-19
Yussuf Buba
Asali: Facebook

"Dole mu dauki matakan kiyayewa da samar da hanyoyin yada sahihan bayanai da kuma zama cikin shirin ko ta kwana tun kafin a samu bullar cutar a yankinmu.

DUBA WANNAN: COVID-19: Mun fara aika wa talakawa tallafin kudi - Ministar walwala da jin dadin jama'a

"Bisa la'akari da duk wadannan abubuwa da na zayyana, ina mai sanar da cewa na sadaukar da gaba daya albashina a matsayina na dan majalisar wakilai domin yakar annobar cutar coronavirus a mazabar Gombi/Honng.

"Wannan sadaukarwa da tallafi zai cigaba har zuwa lokacin da muka tsallake siradin fargabar wannan annoba ta cutar coronavirus," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng